Yadda zaka maida wayarka CCTV camera

Yadda zaka maida wayarka CCTV camera


Assalamu Alaikum warahmatullah


Dan/yar  uwa barkanku Da zuwa shafin Mubarakeey Tv na Internet wato Muhabteam.com a cikinsa muna kaddamar da Muhimman Darussa Da suka shafi Technology da hanyar samun kudi a Internet da sauransu donhaka Bayan ka kammala duba wannan darasin Zaka bibiyar wasu darusan ma saboda na tabbata zasu Amfaneka sosai

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan sabon videon. A yau da yardar Allah zamuyi bayani ne akan CCTV camera. Ta yadda zaka maida wayarka CCTV, Kana kallon bayanan a computer ka.
A wannan darasin zamuyi bayani ne Akan yadda zaka ga a binda ke faruwa a gidanka ko a shagonka ko a kasuwar ka ko a masallaci, a takaice duk Inda yake bukatar Tsaro.

Zaka yi amfani da wani application mai suna ip webcam. Zaka dauko wannan application din a play store bayan ka dakko shi sai ka shiga cikin application din.

Hanyar da zaka yi wannan Aikin


Abu na farko da zaka fara shine zaka bawa application din damar Aiki a wayarka. Sai ka bude application din ka nemi inda zaka dau IP address din Application din bayan ka dakko sai ka saka shi a goggle chrome din ka (ma’na cikin computer ka).

Bayan ka sa shikke nan zaka fara ganin abinda ke faruwa a gurin da kake so, amma sai ka kai wayar taka inda ka ke so ka ga abinda ke faruwa.

Zakayi controlling din wayar taka ta computer, zaka iya juya camerar zuwa camerar gaba ko ta baya, zaka iya Karo volume da wasu sauran ayyukan.

Dan uwa idan ka kalli wannan videon zaka fi gane duk abinda muke nufi.Wannan shine link din Camera da zaku dauko:
Mungode sosai da ziyartar wannan shafi namu da kayi sannan ka bada lokacin ka wajan bincike a cikinsa Muna faka fatan Alkhairi sannan muna Adduar Allah yasa shigowar da kayi Ta amfaneka.

muna rokonka kamar yanda ka amfana da wannan maudui ka temaka ka yadashi a facebook ko whatsapp group ko twitter ko kuma kowanne kalar social media don ka amfani abokan ka dashi 

idan kana da tambaya ko shawara ko karin Bayani zaka iya rubuta mana a kasa agun comment insha Allah zamu amsa maka cikin sauki


Wassalamu Alaikum mungode.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-