Yanda zaka hana a dameka da kira ta wayarka

Yanda zaka hana a dameka da kira ta wayarka


Yanda zaka hana a dameka da kira ta wayarka


Assalamu Alaikum warahmatullah


Dan/yar  uwa barkanku Da zuwa shafin Mubarakeey Tv na Internet wato Muhabteam.com a cikinsa muna kaddamar da Muhimman Darussa Da suka shafi Technology da hanyar samun kudi a Internet da sauransu donhaka Bayan ka kammala duba wannan darasin Zaka bibiyar wasu darusan ma saboda na tabbata zasu Amfaneka sosai.

Wannan darasin yana da muhimmanci sosai saboda zai baka damar ka hana kowa kiranka ko kuma ka zabi wanda kake so ka hana, akwai hanyoyi da yawa da zaka iya yin Hakan amma a yau zamuyi bayani ne Akan wani muhimmin application mai suna (priority contact).

Hanyar yin wannan Aiken shine Kamar hana:


Da farko zaka dauko wannan application din mai suna a sama a play store, bayan ka dakko sai ka shiga cikin application. Application yana da sauki sosai, bayan ka saita application din(maana ka bashi damar aiki a wayarka) kawai sai ka zabi number da kake so. Misali wata number kana so kayi blocking dinta wata number kuma Hutu zaka bata. 

Abu mai muhimmanci a wannan application din shine, zai Baka damar ka kashewa number sauti( in number ta kiraka wayar taka bazata yi Ringing ba”Kara”).

Na tabbatar da idan ka kalli wannan videon zaka ji dadin wannan Application din.

Videon mu na yau zai magana ne akan yadda zaka sarrafa lambobinka na waya.
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Wannan shine link din da zaku shiga.


Mungode sosai da ziyartar wannan shafi namu da kayi sannan ka bada lokacin ka wajan bincike a cikinsa Muna faka fatan Alkhairi sannan muna Adduar Allah yasa shigowar da kayi Ta amfaneka.

muna rokonka kamar yanda ka amfana da wannan maudui ka temaka ka yadashi a facebook ko whatsapp group ko twitter ko kuma kowanne kalar social media don ka amfani abokan ka dashi 

idan kana da tambaya ko shawara ko karin Bayani zaka iya rubuta mana a kasa agun comment insha Allah zamu amsa maka cikin sauki

Mungode.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-