Yanda zaka iya cirewa kowacce kalar waya security cikin sauki
Assalamu alaikum en uwa barkanmu da sake saduwa daku a sabon
videon mu nayau kamar yanda muka muku bayani zamu koya muku yanda zaku iya sire
kowanne kalar security a wayoyinku .
Menene security
Security shine abin da muke sakawa wayoyin mu don kare
kawunanmu daga masu shige-shige a waya ko kuma idan barawo ya sace zaa ji
saukin ganoshi yanzu haka security ya zama daya daga cikin jerin abubuwan da
kowanne me waya yake amfani dashi don ganin yak are wayarsa.
Nauukan tsaro
Akwai nau ukan tsaron waya wato security kala-kala wanda
mutum ze iya amfani dasu tin daga kan mafi girman tsaro izuwa izuwa mafi saukin
tsaron Amma kowanne da kalar amfanin sa sannan da muhimmancinsa da kuma lokacin
daya dace muyi amfani dashi .
Matsalar tsaro
Babbar matsalar da take faruwa damu bayan mun sanya wa
wayoyin mu security wato tsaro shine mantuwa da yawa daga cikinmu muna manta Kalmar
da muka saka.
Ko kuma wani daga cikin yara ko en uwa yakan dauki wayarmu
yayi latsawa harse ya saka adadin da company ya bada damar a saka wanda hakan
yake janyomana asarar wayoyin mu wasu lokuta bayan sun kulle kansu musamman
wayoyi masu tsada irin su iphone da sauran su .
Me ya kamata Kayi
Bayan wayar ka ta shiga security taki fita saboda matsalar
da aka samu na mantuwa ko kuma na yawan dubawa da jamaa sukayi hanya biyu ne
kode kaje gun masu computer wanda wannan shine mataki na karshe amma wannan
yana faruwa ne idan Allah yasa wayar takai matakin da baa soba.
Mataki na biyu
Shine zaka iya budeta da kanka ta wani dan karamin dabaru da
aakeyi wanda da yawa sunsani wasu kuma basu sani ba don haka yanzu muka kawo
muku hanyar da zata temaka muku wajan ganin kun cire security daga wayoyinku ta
hanya me sauki cikin kwanciyar hankali
Wannan shine cikakken darasin video na yanda akeyi zaku iya
shiga ku kalla dalla-dalla
Wannan shine link din channel din data dauka nauyin videon :Danna nan
Daga karshe muna muku godiya da bibiyarmu da kukeyi sannan
idan kuna da tambaya zaku iya mana comment anan nake ce muku assalamu alaikum .