Yanda zaka gano password din ko wani Wifi
Assalamu alaikum, barkanmu da saduwa daku wannan sabon darasinnamu na yau mai taken (Gano password din kowani wifi. Muna fatan wannan darasin zai amfane mu baki daya.
Abu mafi muhimmanci da ya kamata kayi shine:
Kafin ka samu damar samun password na kowani wifi sai kabi wasu
hanyoyi wanda zasu iya zama masu sauki wasu kuma masu wahala, amma mu munne
muku hanya mafi sauki da zaka gano.
Wasu hanyoyi ake bi don ka sami password na wifi?
Hanya ta farko( amsar password daga gurin mai shi)
Wannan hanyar tafi kowace hanya dadin sha’ani, saboda a
wannan hanyar bakayi ha’inci ba ko nace baka dau abinda b aba naka ba. Kuma ko
da mai shi ya canza password din zaka iya tambayar sa ya sake saka maka.
Hanya ta biyu ( Amfani da wasu Application na Android)
Wannan hanyar tafi kowacce hanya matsala. Saboda in ka shiga
play store zakaga Application akan (hacking din password na wifi) sunfi dubu. Kuma
a iya binciken da mukayi bamu ga wani Application wanda yake wannan ba, na
gwada Application sunfi goma, amma kash ba wanda yayi, masana a bangaren sun
tabbatar min ba wanda yake yi kuma ba wanda zaiyi. Dan haka dan uwa karka wahalar
da kanka akan meno wani app a play store don yayi maka wannan aikin. Indai ba na kudi bane.
Hanya ta uku ( Amfani da ta hanyar wanda aka bawa password )
Wannan hanyar ita zamuyi Magana akanta, tana da dan wahala
saboda bako waccece take yi ba. Misali akwai wasu app da sukeyin hakan akwai
kuma website da.
A sawa naka password
Ka tabbatar wannan wifi din an taba sawa wani naka, ma’ana ansawa
wani wifi din, saboda da wayar tashi zakayi amfani don gano password din wifi.
Wani website zakayi amfani dashi
Website din da zakayi amfani dashi shine
Domin samun cikakken bayani a aikace ka kalli wannan videon
zaka gane komai a karamin lokaci