Yanda zaka iya bibiyar danka ko matarka ko kuma Yarka ko mijinki cikin sauki.
Assalamu alaikum en uwa barkanmu da haduwa daku a wani Bayani da zamuyi
muku yau wanda yana da matukar muhimmanci ga dukkan masu nauyi a kansu na
tarbiyya ko miji ko mata ko uba ko uwa.
Tinatarwa
Irin wadannan application da suke zuwa a duniya kullum da kuma bayanansu
da mukeyi ba wai munayi bane don a samu taasa a cikin Alummah munayine kawai
don wayar dakan alummar mu musamman wadanda Allah ya daurawa nauyin tarbiyya a
kansu saboda lokaci da dama zaku iya ganin mahaifi ko mahaifiya suna tsoron
siyawa yaransu naurar zamani saboda gudun lalacewa duk da cewa yanzu haka
sunzama dole a zamanin da muke ciki .
Faida
Muna irin wadannan bayanan ne kawai don iyaye wanda nauyin tarbiyya yake
kansu su samu damar saukeshi cikin sauki ta hanyar da Allah ya umarcesu sannan
kuma kuma ku san cewa akwai wannan abu a duniya ta yanda koda wani ya muku don
niyar cutarwa zaku iya ganewa.
Darasin yau
Ayau zamu kawomuku wasu Application ne guda hudu da zasu temaka muku
wajan ganin kun bibiyi yaranku ta hanya me sauki kuma ta yanda ya dace koda
sunyi nesa daku donhaka ba tare da bata lokaci ba muje mu fara
Application na daya
Application me suna Footprints
Shi ampaninsa ze baka dama kana bibiyar duk inda danka yake sannan kasan
cewa ya isa inda ya nufa , tare da amfani da tsarin GPS , bayan ka hada wayarsa
ko agogonsa da application din.
Idan application din ya burgeka danna nan kayi download
Application na biyu
Application me suna FamilyTime
Shi amfaninsa ze baka dama kana bibiyar dukkan kiran da kuma sakonnin da
danka yake turawa ko a turomasa sannan zaka iya tseda wasu application din da
bakaso yayi amfani dasu da websites din da baka so ya shiga sannan Application
zena fadamaka cikakken lokacin da danka yake batawa a waya sannan ze baka damar
bibiyarsa.
Idan application din ya burgeka danna nan kayi download
Application na uku
Application me suna NetNanny
Wannan application yana da matukar amfani saboda yana amfani ne da artificial
intelligent wajan goge duk wani abu da yake zargin be dace da danka ba na
fitsara ko kuma taaddanci sannan zena sanar dakai lokacin da da danka yake
batawa a waya kuma zaka iya control din lokacin sannan zena sanar dakai duk
wani search da danka yayi a internet.
Domin download din wannan application danna nan
Application na hudu
Application me suna OurPact
Shi amfaninsa ze baka dam aka goge duk application da baka yarda dasuba
a wayar danka sannan zaka iya sanya iya website din da zena shiga sannan zaka
tsara lokutan abubuwansa na rana misali lokacin da yake bacci idan yayi wayar
ta dauke sannan kuma abu nagaba ze baka dama kana dauke internet wayar danka a
wasu lokutan da kake so kamar lokacin makaranta.
Domin download din wannan application danna nan
Gargadi
Daga karshe muna sanar da en uwa cewa wannan bayani munyi shine badon
komAI BA SEDAN TEMAKO DA KUMA wayar da kan alummar mu donhaka duk wanda yayi
amfani dashi ya cuci wani mude ba da yawunmu ba.
Wannan shine karshen bayanin anan nakecewa wassalam kada ku manta yin
comment idan kuna da tambaya.