Bayani Akan kalolin Application din daya kamata kowa yana kula dasu a wayarsa
Assalamu Alaikum warahmatullah en uwa barkanmu da wannan lokaci
Kamar yanda muka sani tin lokacin da wayoyin hannu suka fara bayyana suke ta samun ci gaba tare da ci gaban zamani ta yanda yanzu sunzama kusan suna hanya mafi saukk ta saduwa da kowanne kalar dan Adam.
Yanzu kowanne kalar company zakaga kokarinsa yayi website kk Application daze bawa jamaa masu wayar hannu damar shiga shagonsa ko kasuwar sa dayin siyayya cikin.
kai hatta bangaren wasanni ma irin su kwallon kafa da sauransu zakaga suna kokari wajan suga sun hadu da alumma ta hanyar waya ko hukuma ko kuma wasu maaikatu ko bankuna ko asibitoci.
To don haka wasu bata gari suke amfani da wannan dama suke hada wasu Application don su cutar da Alumma dasu ko kuma su saci bayanan mutum sannan su seda wa company don samun kudi shikuma a dameshi da talla a wayarsa.
Illolin Application din a waya
Irin wadannan Application suna saka waya zafi ta yanda cpu dinta ze kasa daukar damar ayyukan daya saba daga karshe ta fara tsayawa ko hakan yakai ga mutuwar battery, ko kuma wani sain su saka wayarka tana abubuwa wanda zaka zata ta lalace amma kuma ba abin daya sameta kamar daukewa tana aiki da sauransu.
Kala Na Daya
Application Masu Nauyi
A wasu lokutan za kana iya ganin wayarka ta dauki zafi A yayin da kake amfanj da wasu nauukan Application din musamman a bangaren games, Wannan yana nuna maka cewa wayarka bata cika sharudan bude wannan game ba ko kuma Application kamar ka mata dolene donhaka se kayi kokarin Sauke shi saboda yawan Amfani dashi ze iya kashemaka waya
Kala na Biyu
Application masu hada Application da yawa
Misali : irin Application din da zakaga sun hada whatsapp da Facebook da Twitter a Application daya wai don a saukaka maka wajan samun abin da kakeso a waje daya, to amma irin wadannan Application suna da matukar illa wajan satar bayanan mutum a cikin wayarsa be saniba shiyasa za kaga ana yin su da design masu kyau don suja hankalin jamaa, donhaka ku nesanta dasu sannan kuyi kokarin Amfani da Application na asali.
Kala na Uku
Application masu enci
Akwai wasu nauukan Application da za kaga idan kazo install dinsu a cikkn wayar ka zakaga suna neman abubuwa har wanda basu dace da aikinsuba,
Misali idan kayi download din Application wanda aikinsa akan edit na hotone kawai a wajan install sekaga yana neman izinin wajan kira dana sako da map da sauransu wanda a kaida be kamata ya ne mi sama da camera ba.
irin wadannan Application suna da matukar hadari a gareka da wayarka.
Kala na Hudu
Application Masu Talla
Application masu yawan Talla zasu iya zama hadari akkan bayanan wayarka, da yawanmu basa kula da wannan matsala da take faruwa Company da suke talla a Application din suna da enci irin na Application din suna iya shiga hotuna da video na wayarka sannan su kwaso bayanai.
wadannan sune kadan daga nauukan kalar Application masu hadari akan wayoyinmu donhaka amuyi kokari mu kula sosai donganin munkare wannan shine karshe idan kuna da tamabaya zaku iya tuntubanmu agun comment anan naake cenuku assalamu Alaikum