Applications da zasu temaka maka wajan kare wayarka daga sata.


 

Applications da zasu temaka maka wajan kare wayarka daga sata.


Assalamu Alaikum warahmatullah en-uwa barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri.

kamar Yanda kuka gani a tittle yau za muyi bayani ne akan babbar matsala da take damun kowa tin farkon shigowar wayoyin zamani wato satar waya ko kuma binciken sirrin ka.

Kamar yanda muka sani Yanzu haka wayoyin hannu na wannan zamani sun zama daya daga cikin jigogin rayuwar da yawa daga cikinmu basa iya jindadi idan sukayi nesa da wayoyinsu saboda yanda suka taallaka komai nasu da wayartasu.

Tin farkon fitowa waya da yawa daga cikin Alumma suka dauketa a matsayin dan uwa ko aboki ko miji ko mata saboda duk sirrikansu da suke mutane ajiya kamar zantuka da takaddu da kuma abin daya shafi muamalar kudi yanzu sunhade sunbawa wayoyinsu.

shiyasa duk lokacin da wani ya saci ko kuma taba wayarsu ze iya rabasu da wasu muhimman abubuwa a rayuwarsu ko kuma mutum ya duba sirrin da be kamata ya ganiba wanda watakila ya cutar dashi me wayar musamman sirrikan dangi da en uwa.

Donhaka aka kawo wadannan Application don su bada gudunmawa sosai wajan kare wayoyin jamaa daga masu yawan shige--shuge da kuma sata.


Application na Daya


sunansa Don't Touch My Phone


Zaka iya amfani dashi domin ya temaka maka wajan kula da masu sata ko kuma en sa ido, Ta yanda zena bayyana wani sauti me karan gaske duk lokacin da wani ya taba wayarka, musamman ma idan akace tana Aljihunka ko kuma cikin jaka ga mata, Sannan kuma zena sanar dakai duk lokacin da wani yayi kokarin saka password don ya shiga wayarka.

Danna nan donkayi download dinsa : download

Application na Biyu


Sunansa Lookout


Wannan Application yana amfani a matsayin anti-virus ko kuma me kula da Application marasa kyau, Yana da tsari na gane wajan inda wayarka take idan ka rasa ta ko kuma ka manta inda ka ajiye ta,, Sannan yana bincika duk wani Application da kayi download don ya tabbatar da ingancinsa, Sannan na kudinsa Yana iya baka damar iya kulle wayar ka daga nesa ko kuma daukar wani Abu a wayarka ko gogewa.

Danna nan donkayi download dinsa : download

Application na Uku


Sunansa Cerberus Phone Security

Application me matukar abin mamaki ze baka damar control din wayarka ta hanyar Internet kk kuma ta hanyar sakon massage idan babu internet, Saboda ya nunamaka me É“arawo yake aikatawa bayan ya saci wayarka, Sannan ze baka damar kana duk kiran da yake zuwa da sakonni da kuma camera dukka ta nesa.

Danna nan donkayi download dinsa : download


Application na Hudu


Sunansa Prey Anti Theft


Wannan Application yana baka dama wajan ka samu dukkan abubuwan da kakeso Ta hanyar ka shiga website dinsu sannan ta ciki kana kula da dukka abin da yake faruwa ya wayarka Ta yanda zaka iya saka wayarka tana dauka maka hoto tana turomaka ko kuma tana turomaka adress din inda take ko bayyana hoto akan screen ko kuma ka saka tayi kara don ka gane inda take.

Danna nan donkayi download dinsa : download


wannan shine karshen Bayanin mu baki daya anan nake ce muku Assalamu Alaikum Mungode
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-