HANYA MAFI SAUKI DA ZAKA IYA KARANTA SAKON DA AKA GOGE A WHATSAPP
Assalamu alaikum warahmatullah en uwa masu bibiyar mu barkan
ku da wannan lokaci sannun mu da sake saduwa daku a wani sabon shiri na yanda
zaka iya karanta sako da ake gogewa a whatsapp.
Kamar yanda muka sani a kowanne second na duniya duniya kara
samun cigaba take na abubuwan da suka shafi naurar zamani da kuma abubuwan da
suka shafi internet ta yanda da yawa daga cikinmu za suga duk application din
da suke amfani dashi yana canjawa lokaci bayan lokaci .
Wannan ya biyo baya neta yanda company technology na duniya
suke rige-rige wajen ganin sunkawo abun da za sufi abokan karawar su jan
hankalin jamaaa donhaka za kaga kokarin kowanne application zuwa da sabon abu.
To shima whatsapp dayane daga cikin irin wadannan company
masu irin wadannan amfanuka na kokarin ganin sunkawo me amfani sabon , shiyasa
zakaga baa cikakken wata 2 se sunzo da sabon update a daya daga cikin update
din da suka kawomana shine goge sakon da aka tura ,
Amfanin hakan
Idan baku mantaaba da baya idan muka rubuta sako a whatsap
muka daga baya muka gano akwai kuskure zakuga bama iya gyarawa sede mu danna
alamar (*) semu rubata kuskuren a gabanta.
Don haka Wasu daga cikin mu zasu iya ganin amfanin wannan
tsari da whatsapp suka kawo sosai ta yanda yake basu dama suna goge kuskuren da
sukayi a rubutu suna gyarashi izuwa dede.
Illar wannan tsari
A maganar gaskiya wannan tsari da whatsapp suka kawo bashi
da wani aibu ko ince illa , amma kuma a matsayin mu na mutane kowa idan yaga
sako anturo be karanta ba angoge hakn yana damunsa wanda zakuga shi kawai
burinsa seya karanta hankalinsa ze kwanta shiyasa abun yake dan damun jamaa.
Shiyasu wasu suka kirkiri Application me suna Notification history log
Amfanin wannan application shine zabaka dama kana samun
dukkan sako na wani sako daya zomaka daga wani social media kamar whatsapp ko
messenger ko twitter sannan koda angoge acan to shi baze gogeba
Ga videon yanda ake amfani da Application din
Danna nan don kayidownload dinsa : download
Muhgode da bibiyar mu idan kuna da shawara ko tambaya ko Karin
bayani ku rubuta mana agun comment insha Allah zaku samu cikakkun amsa Mungode