HANYAR GANO BARAWON WAYA

 


YANDA ZAKA IYA GANO BARAWON WAYARKA KO KUMA DUK WANDA YAKE MAKA BINCIKE A WAYARKA CIKIN SAUKI

Assalamu Alaikum warahmatullah Jamaa Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri.


A yau kamar yanda kuka gani a tittle din wannan rubutu cewa zan mana bayani ne akan wani Application me matukar muhimmanci wanda kowa a cikinmu Yana da bukatar ace Ya sanya shi a wayarsa saboda hakan ze temaka matuka wajan kare wayarsa daga mutane masu sata ko kuma leken asiri.

Game da Application


kamar yanda muka sani tin farkon zuwan wayoyin zamani masu amfani da Technology da yaci gaba ake samun cigaba na Application da yawa wanda wasu jamaa ke kirkira don saukaka maana rayuwa a kowanne bangate.

Donhaka a bangaren kula da sirrikan waya ma musamman ga mutane masu son ganin asirinka ko barayi akwai Application da yawa da zasu temaka maka wajan ka kare kanka daga wannan bangaren., wasu daga cikin suma munyi bayanin su a channel dinmu ta youtube me suna mubarakeey tv idan kuna shaawar ku leka ku gano, amma kamar yanda kuka sani a komai akwai wanda yafi shiyasa muka zabo muku wani muhimmin Application me suna lockwatch saboda cancantarsa.


Me yakeyi

wannan Application me suna lockwatch yana abubuwa da yawa wanda muke da matukar shaawar su a cikin wayoyinmu misali duk wanda ya dauki wayarka zeyi kokari ya maka hotonsa ya tura maka ta email sannan ze iya dauka maka records na magana da kuma location din mutumin daya dauki wayarka inda yake sannan Application din yana da bangare biyu akwai na kyauta akwai na kudi, amma iya na kyautar tasa ma ze iya biya maka dukkan bukatun ka shiyasa ma muka zabeshi.

Saboda yana da dukkan abin da akeso na kulawa musamman bangaren bayanan ka na sirri da kuma sauran abubuwa daya kamata ya kula maka dasu a wayarka.

Yanda ake amfani dashi

kamar Yadda muka sani amfani da Application dinnan abune me matukar sauki bayan kayi download dinsa ta link din da zamu ajiye a kasa zaka bude Application din daga nan se mutum ya danna Alamar kunnawa bayan nan seya zabi Email din da yakeso ana turamasa sako, daga nan shikenan ya seta Application din ze fara kaimasa hotunan duk wanda sukeso su taba masa waya.

Wannan shine videon cikakken Bayanin applications din
Wannan shine link din Application din daza ku dauko: DANNA NAN

Mungode sosai da bibiyar mu da kukeyi idan kuna da
tambaya ko karin bayani zaku iya Rubuta mana su a gun comment.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-