Sabon WhatsApp mai yin komai da kansa

Sabon WhatsApp mai yin komai da kansa

Sabon WhatsApp mai yin komai da kansa


 Assalamu Alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da warhaka, dafatan mun sake saduwa da ku cikin aminci.A yau da yardar Allah zamuyi bayani ne akan wani muhimmin Application wanda kowa yake amfani dashi, mai suna Whatsapp.

Bayani akan WhatsApp na Asali.

Kamar yadda muka sani ankirkiri WhatsApp ne a shekarun baya, kuma yasamu amsuwa a gurin jama'a, a yanzu yana daya daga cikin Applicationa wanda akafi amfani dasu a duniya. Wannan Application na WhatsApp in kana sanshi kai tsaye zakaje play store na wayarka, bayan ka rubuta sunanshi a take zai zo maka, daga nan sai kayi installation din shi. Zaka iya amfani da normal WhatsApp ko kuma kayi amfani da WhatsApp na yan kasuwa mai suna WhatsApp Business. Duk su biyun suna da abubuwa na musamman wanda mai amfani dasu zaiji dadin aiki da su. Abu na karshe akan WhatsApp na asali shine, duk wasu bayananka zasu adana maka, ta yadda hackers bazasu iya cimma bayananka ba, sannan ba wanda zai kulle maka lanbar wayarka, musamman idan ka saka two-step-verification.


WhatsApp wanda bana asali ba (Na Bogi)


Bayan an kirkiri WhatsApp kuma akaga irin nasarar da ya samu, sai wasu daga cikin mutane suke kokarin su saci fikirar sa. Daga nanne aka kirkiri Gb WhatsApp, WhatsApp plus, da saurasu.


Suna da muhimmanci?


Ea suna da muhimmanci sosai, ta yadda zakuga akwai abubuwa da yawa wanda WhatsApp na asali bashi dashi amma su wadannan suna dashi, misali, themes, canza sunan sa, da sauransu. Zakayi wayanci duk abinda kake so a cikinsa. Dan Haka mutane da yawa suna Amfani da shi. 


Wannan shine link din:

Dannan nan




Mene matsalarsa?

Yana da matsalaloli da yawa, amma zan dauki masu muhimmanci nayi bayani akansu. 

Na farko Rashin tsaro

In kana amfani da WhatsApp wanda bana asali zaka iya samun matsalar satar bayanka, ina mufin hackers zasu iya daukar duk sakunnin da kake yi. Kuma su tuawa wanda suke so.

Na biyu Rashin yin backup

Da zarar ka fara Amfani da wannan WhatsApp din shikke nan baka iya dawo da bayananka ba. Misali, in kana amfani da WhatsApp na asali zaka iya sa yana yin backup a kullum ko sati ko wata, hakan zai baka damar dawo da baya nanka duk lokacin da ka rasasu. Amma shi wanda bana asali ba baiyi, kuma koda yayi lokacin da zaka so ka koma WhatsApp na asali to wannan bayanan naka baza su dawo ba.

Na uku zaka iya Rasa Number ka

Kamfanin WhatsApp na asali da suka fahimci mutane suna satar musu fasaha, sai suka dau matakin rufe duk wata number da take amfani da WhatsApp na bogi. Dan haka in kana amfani da shi, zaka iya rasa lambarka.

Ra'ayina

Zaka iya amfani dashi idan kana da lambobi ya yawa, saboda yana da abubuwa sosai a cikinsa. Amma idan lambarka daya ce kuma samun sabon layi abune mai wahala a gurinka to karkayi amfani da shi.

Yan uwa anan muka kawo karshen wannan darasinnamu na yau , dafatan ya burge ku kuma zai amfane ku. Kada ku manta dayi mana sharing na wannan page dinnamu.


Wassalamu Alaikum.

Mungode.


Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-