Yanda zaka iya gano mutum ta lambar wayarsa

 


Yanda zaka iya gano kowane mutum ta lambar wayarsa

 

Assalamu alaikum warahmatullah en uwa barkan mu da sake saduwa daku a wannan darasi me matukar muhimmanci.

Kamar yanda kuka gani a tittle yau zamuyi bayani ne akan yanda mutum ze iya bibiyan duk wani wanda yakeso cikin sauki ta hanyar lambar wayarsa.

 

Menene amfanin darasinnnan

Da yawa daga cikin mu kowa yasan halin da muke ciki yanzu na harkar social media ta yanda kowanne mutum yake fitowa ya tofa albarkaci n bakinsa a cikin wannan kafa ta sada zumunta to amma mene ne yake jawo a bibiyi mutum

Da yawa sukanyi amfani da wannan kafa ta sadarwa don su ci mutuncin mutm wanda da ace ido da ido ne ba dole su iyaba shiyasa za kaga wasu sukan boye sunayensu suna fadawa mutane dukkan abin da ransu yakeso har takai da sunkai wani ma makura ko kuma ga matakin zuwa gaban hukuma.

 

Menene track

Track daya ne daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajan aga an bibiyi mutum shin don yayi lefi ko kuma don a kula dashi misali idan wani yayi kidnapping ya kira lamba hukuma zasu iya bibiyansa ta hanyar wannan lamba don su kamashi ko kuma mahaifi yana da dansa ze iya amfani da wannan hanya cikin sauki.

 

To me yasa muka zabi lambar waya

Da yawa daga cikin mu sun sani cewa yawancin masu boye abubuwannan babu abin da suke iya bayyanawa alumma face lambar wayar su , shiyasa mu kuma zamuyi amfani da lambar wayar wajan ganosu.

Don haka daga yanzu duk wani wanda ya boye suna ko gari ko hoto a facebook ko whatsapp ko kuma kowane kalar social media yaci mutuncinka ko ya wulakanta wani naka ko kuma yakewa alumma abin da be daceba wannan itace hanya mafi sauki da zaa iya kamashi bashan wahala’

 

Ga video daze koyamaka yanda ake a aikace

 


Ga link din website din :  Danna nan

 

Mungode da bibiyar mu da kukeyi sosai a wannan shafi muna godiya da kulawarku don haka idan kuna da tambaya ko Karin bayani seku tuntubemu a gun comment.

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-