Yanda zaka iya bibiyar wayar danka ko Matarka 2020


 Yanda zaka iya bibiyar wayar danka ko Matarka


Kamar Yanda muka sani kowa a cikinmu Munyi video akan yanda mutum ze iya bibiyar wayar dansa ko matarsa ko mijinta amma kuma da yawa basu gane Yanda videon yake aiki ba ko kuma wasu ya musu aiki daga baya sun rasa ya zasuyi sannan kuma zamani yazo yanzu an samu wani ci gaba akan su wannan Application sannan kuma an samu karin wasu da yawa na sabin application shiyasa muka yanke shawarar kara yin wani video domin mu amsa muku tambayoyinku sannan kuma mu kara kawomuku wasu sabin Application din masu saukin aiki wanda kowa zeji dadinsu.

Tinatarwa


Kafin ka zabi Application din da kakeso kayi ampani dashi a wannan videon kayi kokari ka karanta daga farko har zuwa karshe saboda akwai bayani me matukar muhimmanci sosai a wannan darasi.


Amfaninsu


Shi amfanin wadannan Application na asali anyi su ne kawai don su taimaka wajan mahaifi ko mahaifiya su kula da tarbiyar yayansu namiji ko mace misali wadannan Application zasu baka daka dama ka iya bibiyar duk inda danka yake ko kuma ina yaje ko daga ina yake ko ina zeje.

sannan akwai wanda su kuma zasu baka dama kana control din wayartasa ta yanda za kana iya kashe Internet din wayarsa sannan za kana iya kunnawa hakan zesa kana hana danka shiga Internet a lokacin karatu ko kuma a makaranta ko waje me amfani.

akwai wanda su kuma zasu baka dama kana iya kashe wayar danka lokacin da kakeso sannan ka kunnata lokacin da kakeso ko kuma kasa screen ya dena aiki a kowanne lokaci ta yanda zaka samu damar sakashi bacci da wuri misali zaka iya cewa karfe12 na dare tana yi wayar taa mutu saboda ya kwanta da wuri.

sannan kuma Application din da aikin su shine su baka duk wani bayani akan wayar danka misali awa nawa yakeyi yana game ko kuma tsawon awannin da yake batawa yana chattin sannan zasuna nunamaka dawa yake chat sannan me yake turw.

sannan akwai wanda suma zasu baka dama kana iya gano wannan kalar website danka yake shiga sannan in ya shiga me yakeyi sannan zaka iya hanashi shiga duk website din da baka so ya shiga a wannan yanayi cikin sauki.


Nau-ukan Application din

Irin wadannan Application suna da nauuka da yawa kamar yanda bayanan su ya gabata a baya a bangaren ayyukansu.

sannan kamar yanda suka samu banbanci a aiki dole su samu banbanci a farashi don haka su wadannan Application da muke gani a cikinsu akwai na kudi akwai na kyauta naa kudin suna da yawa sannan na kyauta ma suna da yawa

Banbancin tsakanin su

Su na kudi

sune wadanda zasu baka dama ka gano dukkan abubuwan da kakeso ka sani a wayar wanda kake bibiya manya da kanana tindaga kan inda yake har zuwa kalar chat da sauransu

su kuma na kyauta

sune wanda zasu baka dan abubuwa madede ta wajan yin aiki kamar location da kuma web history.

Wadanne amfani zaka iya dasu


Amfanukan da zaka iya da wadannan kalar Application suna da yawa misali abu na farko daga amfanin su saninsu zesa ka iya kare kanka daga wanda yakeson cutar ka.

abu na biyu

zaka iya amfani dasu wajan gane duk wanda kakeso ka bibiya uwa ko da ko miji ko mata ko ya da sauransu har ma'aikata a wajan aiki dukka ana iya bibiyar su.

Abu na uku

zaka iya amfani da wadannan kalar Application don ka iya bibiyar wayarka saboda koda Allah yasa taa fadi ko kuma wani yayi kokarin saceta kai tsaye zaka iya ganinta cikin sauki sannan koda barawon yayi kokarin format din wayar be isa yayiba.

A cikin su wanne ya kamata ka dauka


Kamar yanda mukayi bayani tin a baya su wadannan kalar Application suna da yawa matuka sannan kuma wasu na kudi ne wasu na kyauta to kuma wasu basu da kudi wasu kuma basu iya sayaba to wanne Application nee ya dace da kowa

akwai application da yazo daga company Google me sana google family link Kamfanin sunyi shine don ya taimaka wajen samun damar hada mahaifi da yaransa Ta hanyar wannan Application zaka iya hade dukkan wasu da kakeso ka bibiya application din na kyauta ne sannan yana bayyana komai yanaa da dadin aiki kuma yana da dadin shaani na tabbata duk wanda yayi ampani dashi ze burgeshi sosai matuka donhaka gashinan a kasa zan ajiyemuku lin ku danna kalmar download don kuyi saukeshi.

Amma applications din kala biyu ne akwai waanda zakka saka a wayarka a matsayin mahaifi sannan akwai wanda zaka saka a wayar da kakeson bibiya a matsayin wayar danka.

Application din wayar ka : Download
Application din wayar 'da : Download

Wasu kalar da zasu temaka

A baya munyi bayanin irin wadannan Application din a website dinnan idan kunaso kuga bayani akan wasu ku danna nan ze kaiku cikin bayanin seku karanta zaku amfana.


Ga cikakken videon darasin idan kana so ka kalla ka gane


Gargadi

Ba muyi wannan videon ko darasin ba don kawai mutane suje suyi ta barna ko suna duba sirrikan jamaa munyishi ne kawai don wayar dakan Al'umma da kuma temakawa iyaye donhaka duk wanda yayi amfani dashi ta hanyar da bata dace ba mu babu ruwanmu




Wannan shine karshen darasin mungode wassalamu alaikum.





Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-