Yanda zaka iya dawo da lambobin ka daka goge ko suka bata ta hanyar facebook.


 Yanda zaka iya dawo da lambobin ka daka goge ko suka bata ta hanyar facebook.


Assalamu Alaikum warahmatullah Jamaa Barkanmu da saduwa daku a wannan darasi me matukar amfani.

kamar yanda kowa ya sani tin lokacin da wayar hannu ta fara yaduwa a duniya babbar matsalar da take cima mutane tuwo a kwarya shine Batan laambar waya.

Da yawa daga cikinmu zakuga muna da lambar waya a ajiye a wayarmu amma wani dalili ya sanya munrabu da ita, misali batan waya ko batan layin waya ko kuma lalacewa ko rufewa da sauransu

shiyasa tin daga wannan lokaci dukka wasu company da suke da alaka da waya tindaga kan masu hada hardware har masu hada software burin kiwa a cikin su yaya zaayi aa samu mafita akan batan lambar shiyasa zakuga kowa a cikin su yanaa kawo hanyoyi da yawa

Misalin kadan daga ciki

Google
facebook

amma mu yau za muyi bayani ne akan hanyar facebook itama ta Google din munyi bayani zaku iya dubawa a channel dinmu ta youtube.

Meyasa muka zabi facebook.


Da yawa za suna mamaki me yasa mutum ze ajjye lambarsa a Facebook bayan kuma ga Google

To amsar a takaice kamar yanda muka sani da yawa daga cikinmu ma ko gmail basu da shi wasu basu san ma yaya ake amfani da gmail ko kuma yaya ake abudeshi ba shiyasa aiki dashi ze iya danbasu wahala.

Amma shi facebook yanzu yakai matakin da da kyar kaga me rike wayar hannu mutum baya da Account a ciki a yankunan mu sede yaro karami ko kuma tsoho sannan kowanne mutum ya iya Amfani dashi cikin sauki don haka shiyasa ajiye number ko dawo da ita ta cikin facebook tana da muhimmanci.

Yanda ake ajiye Number


Da fari cikin sauki mutum ze bude messenger din cikin wayarsa.

Bayan ya bude daga nan a sama bangaren hagu zega hoton sa maana alamar profile seya danna kanta

Bayan nan zega rubutu ka se yayi kasa har seya iso gun da aka rubuta people kawai seya danna.

To yana dannawa zega zabuka guda uku seya shiga na farko wanda aka rubuta Upload Contact idan yana off se ya meda shi on.

Yanda ake dawo da lambobin


Hanyar dawo dasu tana da sauki kuma ta kasu kaso biyu.

Ta daya akwai ta hanyar wannan link din danna nan zaka shiga

bayan ka danna ze bude maka shafi kamar na Facebook se ka saka username dinka da password na Facebook ze kawo maka gun lambobin ka

ko kuma hanya ta biyu
zaka iya komawa messenger dinka kabi dukka matakan da kabi a baya wajan ajiye lambobi amma idan ka shiga people memakon ka shiga na farko seka shiga na biyi wato manage contact

daga kayi haka ze baka damar yanda zaka dawo da komai na lambobin ka.

Domin karin bayani ga videon da ze muku cikakken sharhi akan yanda akeyiwannan shine karshen darasin muna godiya sosai da bibiyar mu kada ku manta da shere mungode.


CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-