Yanda zaka sami subscribers 1000 a cikin yan kwanaki kadan
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wanannan lokacin, kamar
yadda muka fada a darasinmu na yau zamuyi bayani ne akan yadda mutum zai sami
subscriber a kasa da kwana talatin (30).
kamar yadda kuka sani youtube wata hanya ce ta musamman ta
samun kudi online, dan haka zai kasance sai ka dan sha wahala kafin ka cinma
burinka. Kafin na fara bayani gadan-gadan, ina so nayi maka nasiha game da
youtube channel, dole sai da HAKURI da JURIYA zaka cinma burinka. Amma da zarar
kayi gaggawa ko rashin hakuri, shikke nan kayi rabin faduwa.
Dan haka muka kawo muku wasu hanyoyi da zasu tai make ku
gurin cimma burinku a youtube.
Shin samun 1000 subscribers yana da sauki?
Hmmm dan uwa bazan ansa maka wannan tambayar ba, sai a
karshen wannan darasin, domin inka karanta shi zaka tabbatar da amsar da zan
baka.
Hanyoyin da yaka mata kabi sune kamar haka:
Collaboration videos
Dan uwa, a farkon fara bude youtube channel dinka zai
kasance ka sami subscribers kamar 200, wanda abokai da yan uwa suka yi maka.
Daga nan zaka fara kokarin samun sauran 800. Samun subscribers dari takwas ga
wanda yake sabo a bune ba mai sauki ba. Amma yanzu zan sauka ka maka shi da
yardar Allah. Ka sami dan uwanka da yake da youtube channel kuyi video tare
dashi koda ka fishi yawan subscribers, amma in ka sami wanda ya fika yafi.
Amfanin yin hakan shine, idan kuka yi videon kuka dora, subscribers dinsa zasu
zo maka, shima subscribers dinka zasu je masa. Wani zai iya cewa bashi da wani
wanda ya sani da yake da youtube channel, a hakanma baka da matsala zaka iya
zuwa duk channel din da kake so kuyi collaboration da shi, kayi mai comment
sannan a ajiye mai link din channel dinka da kuma number wayarka. Inna tabbatar
maka da idan kayi wa mutum biyar haka zaka iya samun mutum daya, kuyi videon
dare dashi. Kuma fa ba dole sai kun hadu ba, zai iya turo maka videonsa sai ka
hada da naka. Misali in tutorial ne akan wani abu, ko comedy da sauransu.
Rapdtags
Wannan wani website ne wanda zai taimaka maka gurin gano mai
mutanenku suka fiye kalla a youtube. Misali zaka iya rubuta musu kano, kaduna,
jigawa, kai ko wani gari kake, zaka iya rubuta sunan garin domin ka gano me
mutanen garin suka fi kalla. In ya kawo maka sai ka dauke tags din ka saka a
channel dinka. Hakan zai tai maka maka ka kara yawan subscribers. Kuma zaka iya
amfani da wannan website din domin ya hada maka tags na musamman. Wannan
website din yana da matukar sauki, kana shigarsa zaka gane shi. Wannan shine
link din website din.
playlist
Hada playlist a youtube channel dinka abune mai matukar
sauki. Dan haka ka tabbatar kowani kalar video da kake yi a channel dinka kayi
mai playlist. Misali in a channel dinka kana yin videos akan games, tutorial da
nasiha, kaga kowanne sai kayi mai playlist dinsa daban, bangaren games dadan
ban garen tutorial daban nasiha ma haka. Hakan zai tai makawa wanda yake son ya
kalli videos dinka na game daga ya gama kallon videonka wani na game dinne zai
zo masa. Kuma masu kallo zasuna dadewa a channel dinka indai videos din da kake
yi yana burge su.
Tallata channel a social media
Wannan hanyar ita ma tana da matukar amfani sosai, saboda
zata taimaka maka gurin sanuwa a gurin mutane da yawa, misali sharing din
videos dinka a shafuna na facebook, status na whatsapp da Instagram. Inka dage
ka jure zaka ji dadin wannan hanyar. Zaka iya sharing din links na videos dinka
a gurin comment na shahararrun mutane. A wannan hanyar zai iya kasance wa kana
jin kunyar mutane su ganka kana sharing a kowani pages na facebook, harma da
gurin comment, domin kaucewa hakan (ka kirkiri sabon facebook account wanda
dashi zaka na dukkannin al’amuranka).
Tallata channel a youtube
Zaka iya bawa wanda yayi suna a youtube domin ya tallata channel
dinka. Amma ka tabbatar da wanda zai iya maka tallan irin mutanensa ka ke so
(shigen abu guda kukeyi). Kuma zaka iya sa wani ya tallata channel dinka a
Instagram ko facebook idan ya kasance yana da jama’a sosai.
Yanzu ne lokacin da ya dace na amsa tambayarka: samun
subscribers 1000 a youtube abune mai sauki idan kana da HAKURI da JURIYA.
Musannan in kabi wadannan hanyoyin da nayi bayani akansu.
Muna fatan wannan karamin darasinnamu zai amfanar da yan uwa
da suke son fara samun kudi a youtube. Muna yi muku fatan nasara a duk
al'amuranku.
Anan muke ce muku wassalamu alaikum. Karka manta dayi mana
sharing
mungode.