Application din da yake yin kowai na whatsapp
Assalamu Alaikum warahmatullah yan uwa barkanmu da wannan lokaci da fatan kuna lafiy. kamar yadda muka rubuta yau zamuyi bayni ne akan wani muhimmin Application wanda yake yin komai na whatsapp, ta yadda daga yau zaka goge duk wani Application dake amfana dashi akan whatsapp.
Abubuwanda wannan Application din yake dasu.
Sakon da aka goge
Da wannan Application zaku iya karanta duk sakon da aka turu maka sannan aka goge shi. kamar yadda muka sani a kwana kin baya in kana bukatar yin hakan dole sai ka samo wani Application din, amma yanzu wannan Application din zaiyi maka wannan Aikin, cikin Sauki.
Status saver
Duk acikin wannan Application din zaku iya dakar duk status din wanda kuke so, ba tare da ya turo maka wannan status din ba. zaku iya daukar Hotuna ko bidiyo ko Audio, indai an dora a status na whatsapp.
Whatsapp cleaner
A wannan app zaku iya doge duk wani abu da bakwa so, misali : sau da yawa mukanga wasu hotuna a wayar mu wanda bamusan ta inda suka zo ba, to da wannan Application din zaku iya goge duk wani abu da aka turo maka ta whatsapp.
Whatsapp Web
zaku iya daukar whatsapp dinku daga wanna wayar zuwa wata wayar, in kayi amfani da wannan hanyar. kaga daga yau kade na amfani da wani App din da zaiyi maka hakan.
Fake Chat
Duk a cikin wannan Application zaku iya hada chat na karya, watakila kana san ka tsokani abokinka ko kawarka zaka iya amfani da wannan Application.
Sunan wannan Application din shine WABOX
wannan shine link din sa
Muna fatan darasin yau kunji dadinsa da wannan muke ce muku Wassalamu alaikum. kuma wannan Application din yana da abubuwa da yawa wanda bamuyi bayanin su ba.
Mu hadu a sabon darasi.
Mungode