APPLICATION DIN DA ZAI TAIMAKA MAKA GURIN SAITA RAYUWARKA
Assalamu Alaikum warahmatullah Jamaa Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri.
A yau kamar yanda kuka gani a tittle din wannan rubutu cewa zan mana bayani ne akan wani Application me matukar muhimmanci wanda kowa a cikinmu Yana da bukatar ace Ya sanya shi a wayarsa saboda hakan ze temaka matuka wajan ka kare lokacinka.
Abun da ya kamata ka sani game da Application
kamar yanda muka sani tun farkon zuwan wayoyin zamani masu amfani da Technology da yaci gaba ake samun cigaba na Application da yawa wanda wasu jamaa ke kirkira don saukaka maana rayuwa a kowanne bangate.
Bangare na biyu: Mutane da yawa muna amfani da Applications wanda muke amfani dashi na yau da gobe, kamar whatsapp, Facebook, Twitter, Instagram da sauransu. Amma wasu na amfani da wadannan Apps ta hanyar da bata dace ba, domin zaka mutum ya kan iya cinye Rabin rana da wadannan apps din ba tare da ya amfana da wani abu ba. Hakan kuma bai dace ba ga wanda yake san yayi nasara a rayuwarsa ta duniya da lahira.
Me yakeyi Application din:
wannan Application me suna Glan yana abubuwa da yawa wanda suke da matukar amfani. Amma banban amfaninshi shine xaka amfana da lokacin da kaso, zaka iya sama da minti 30 ko kasa da haka ko sama da haka domin ya fara lissafa maka, kuma wani abun burgewa a wannan Application din shine yana da wasu sautuka wanda yawancin mutane suna bukatar su misali ( Sautin saukar ruwan sama ko sautin jirgin kasa) zaka iya kunna su domin kayi abinda kake so a lokacin da kake son amfani da Application din cikin kanciyar hankali da nutsuwa.
Yanda ake amfani dashi
kamar Yadda muka sani amfani da Application dinnan abune me matukar sauki bayan kayi download dinsa ta link din da zamu ajiye a kasa zaka bude Application din daga nan se mutum ya danna Alamar kunnawa(ma'ana ya bashi damar aiki a yawar) bayan nan shikke nan zai kawo maka fuskar Application din.
Wannan shine videon cikakken Bayanin applications din
Wannan shine link din Application din daza ku dauko:
Mungode sosai da bibiyar mu da kukeyi idan kuna da
tamba
ya ko karin bayani zaku iya Rubuta mana su a gun comment.