Daga yau andena ganin sirrin wayarka

 
Daga yau andena ganin sirrin wayarka

Daga yau andena ganin sirrin wayarka


Assalamu alaikum,yan uwa barkanmu da wannan lokacin. A darasinmu na yau munzo muku da wani Application mai matukar Amfani wanda ya kamata kowa yana amfani da shi.


Amfaninsu


Wannan Applications din zasu taimaka maka gurin ajiye duk wani sirri da kake dashi a wayarka ta Android ba tare da wani ya gani ba. 


Application ma farko (WTMP)


Zaka iya amfani da wannan app din domin sanin duk wanda yayi kokarin bude maka wayarka, zai daukar maka photon wanda yayi kokarin bude wayar, sannan zai fada maka duk abinda yayi a cikin wayarka. Misali idan ya shiga wani application kamar whatsapp ko facebook ko instagram, duk zai fada maka ta yadda zaka dau mataki. Akwai wannan application din a play store domin yin download dinsa Danna nan


Danna Nan


Application : photo to pdf


Wannan Application din yana da matukar amfani domin zai baka damar tura duk abinda kake so a sirrance, misali idan kana so katurawa abokinka photo zaka iya tura masa ta wannan hanyar , sannan ka sakawa photon Security ta yadda ba wanda ya isa yaga abinda yake ciki sai wanda ka fadawa password din. Wannan application din akwai shi a play store , ka danna nan domin download dinsa


Danna Nan



Yanda zakayi amfani da wadannan Apps 


Zakaje play store kayi download dinsu.

Bayan ka gama download dinsu kai tsaye zaka shige su, zasu tambaye ka ka basu damar aiki a wayarka  bayan ka basu damar kai tsaye zaka fara amfani dasu.


Dafatan kunji dadin wannan darasin , kuma insha Allah zai amfane ku.

Wassalamu Alaikum.

Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-