HANYOYIN SAMUN INGANTACCIYAR LAFIYA A LOKACIN SANYI
_________________
A cikin shirin na yau, za kuji Hanyoyi 7 da mutum zai bi don inganta lafiyarsa lokacin sanyi
1. Sanya kaya masu kauri don samun dumi ga yara da kuma tsofaffi. Shan ruwa mai yawa, a kalla lita daya da rabi zuwa biyu a kowacce rana.
2. Sanya Gilashi don kare idanu da kuma abun rufe hanci da baki don kariya daga kura.
3. Shafa mai a jiki don hana bushewar fata.
4. Shafa mai a lebe da kuma kasan kafa, hakan yana hana wuraren fashewa.
5. Idan mutum na da cutar asthma, a rage shiga waje mai datti ko mai kura kuma a kasance da inhaler don halin ko ta kwana da mutum zai iya shiga.
6. A wanke danyen abinci kamar kayan marmari da na lambu kafin a ci don gujewa yaduwar kwayoyin cutuka.
7. Kada a raina atisaye komai kankantarsa. Yana taimakawa wajen narkar da kitse tare da tabbatar da jiki na aiki yadda ya dace. Hakan kuwa na samar da dumi wanda ke daidaita zafin jiki lokutan sanyi.