Me yake faruwa a zaben Niger
🗞 🇳🇪 A jamhuriyar Nijar, yayin da ake tunkarar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrerun wannan shekarar ta 2021, jam’iyyun kawancen da suka mara wa dan takarar PNDS Bazoum Mohamed sun kara jaddada matsayinsu don ganin dan takarar ya lashe zaben.
A sanarwar da suka fitar ranar Litinin a cibiyar jam’iyyar PNDS Tarayya, shugabannin jam’iyyu 45 mambobin kawancen "Coalition Bazoum Mohamed 2021" sun jinjinawa magoya bayansu saboda yadda suka fito suka bai wa dan takarar wannan kawance kuri’un da suka bashi damar zuwa sahun gaba cikin ‘yan takara 30 da suka fafata a zagayen farko.
Bazoum Mohamed ya yaba da kokarin wadannan jam’iyyun duk kuwa da cewa ba a cimma gurin lashe zabe ba tun a zagayen farko kamar yadda aka yi fata.
Jam’iyyun na kawancen "Coalition Bazoum 2021" na ganin akwai alamun samun galaba a zagaye na biyu bisa la’akari da nasarorin da ‘yan takarar jam’iyyun kawancen da ke mulki suka samu a zagayen farko.
Bazoum Mohamed ya ce ya na da kwarin gwiwar samun hadin kan jam’iyyun kawancen na PNDS Tarayya.