Karatu kyauta a Turkey

 Karatu kyauta a Turkey


Karatu kyauta a Turkey


Assalamu Alaikum warahmatullah yan uwa barka da warhaka. A yau munzo muku da hanyar da zakuje Turkey 🇹🇷 karatu kyauta.


Yana da kyau ka/ki karatanta wannan rubutun saboda dashine zaku gane komai. 


Kamar yadda kowa ya sani karatu a kasashen waje yasha ban-ban da karatu a kasashen mu. Kuma mutane da yawa suna bukatar suga sun sami damar yin karatu a kasashen waje amma wasu basu da dama, wasu kuma suna da ita amma basu san hanyar da zasu samu ba. Dan haka da Yardar Allah zamu fada muku hanyar da ta dace ku sami wannan damar tayin karatu kyauta a Turkey.


Me yasa zakaje Turkey karatu?


Wasu makarantun suna bada abubuwa kamar haka:


1.  Karatu kyauta : 


A irin wadannan makarantun suna kokari subawa dalibi karatu kyauta kuma kowani kalar karatu ne kamar su (Medicine, Engineering da sauransu) 

2. Gurin kwana kyauta :

 Yawancin  makarantun suna bada gurin kwana (Hostel) Saboda idan mutum yace shi zai biya wa kansa ba lallai ne ya iya biya ba saboda tsada, dan haka makaranta zasu baka gurin kwana. 

3. Kudin kashewa :

 A bangaren kudi basu da matsala, shi yasa suke biyan kowani dalibi duk wata, kuma kudin zai isheka dai-dai misali. Da kudin zaka siyi abinci, kaya, sabulu, da sauransu. Amma idan kana da kashe kudi sosai to kudin ba zai isheka ba. 

4. Kula da lafiyarka :

 Bazasu barka kaje ba, batare da sun tabbatar da lafiyar ka ba. Domin basason wanda yake da tsutar da zata iya shafar mutane da yawa. Dan haka dole sai sun duba lafiyar ka sannan zakaje. Amma bayan kaje abinda ya shafi lafiyar ka tana gurinsu, zasu baka magani, zasu kaika asibiti idan baka da lafiya, da sauransu. 

5. Kudin jirgi : 

Sune zasu biya maka kudin jirgin da zaka je kasar (Turkey 🇹🇷) da kuma na dawo wa.


Mai suke bukata a gurinka /ki


Abu biyu kwai suke bukata :


1. Maki (Marks) : 

Dole sai ya kasance kana da maki mai kyau a jarabawarka ta Secondary (école secondaire). Kamar 9 credit kuma sukasance C4 zuwa A1. 

2.  Shekaru : 

Basa daukar wadanda suke da shekaru da yawa, wadannan sune shekarun da suke nema


1. Karkayi sama da shekara 20 idan kana son Degree (Diplôme).
2. Karkayi sama da shekara 30 idan kana san Masters degree (diplômes de maîtrise).
3. Karkayi sama da shekara 35 idan kana san PHD.


Idan kana da shekaru zaka iya rage su idan kaje yin passport.


Domin cike wadannan makarantun wannan shine link din


Link din

Link din

Link din

Wannan shine link din da zaka fara cikewa

Wannan shine link din 

Bayan ka danna zai kaika website dinsu wanda zaka ga dukkan sharudan su da kuma dukkan makarantun da suke bada damar yin karatu kyauta. Kuma kowacce makaranta da kagani tana da nata sharudan (Saboda sharudan kowacce makaranta suna ban banta). 

Ga cikakken video nan na Yanda ake Apply

Shiga nan

Shiga nan

Shiga nan

Shawara

Idan kana san cike wa, ka bawa wanda san harkar san harkar sosai, domin kada ku sami matsala. In baka samu ba kacike da kanka amma ka kula sosai.


Ina fatan zaku amfana da wannan damar da tazo muku. Muna yiwa kowa fatan Nasara. A nan muke ce muku mu hadu a darasi na gaba.


Mungode

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-