ME YAKE KAWO MAIKON FUSKA{OILY SKIN}?

 


ME YAKE KAWO MAIKON FUSKA{OILY SKIN}?


_______________________________________


Daya daga cikin hikimar halittar fata a jikin dan Adam dama sauran halittu shine don su baiwa jikin kariya. Ita fatar dan adam itace take rufe tsokar jiki, jijiyoyi, da sauran muhimman sassan jiki.


Kasantuwar cuɗanyar ta da muhalli, sai ta kasance tana dauke da wani irin ƙaƙƙarfan garkuwa wanda yake kare jiki daga hadarin raguwar ruwa a jiki da Kuma shigar wasu ƙwayoyin cuta.


Game da dalilan da yasa fatar dan Adam take yin maiƙo kuwa, ga kadan daga cikinsu sune;


1- Gado: Idan ya kasance mutum yana dauke da sinadarin halitta a jikin sa wanda ya gada daga iyayen sa, wanda yake da alaƙa da wannan matsalar, to akwai yiwuwar shima fatar sa ta rika fitar da maiƙo fiye da ƙima!


2- Canjin yanayi; Kamar yadda muka sani, yanayin zafi yafi yanayin sanyi sanya fatar jikinmu tayi maiƙo fiye da ƙima.


3- Shan wasu magunguna; Yawancin mata masu amfani da magungunan ƙayyade iyali(family planning) suna da yiwuwar su ga fuskar su tana yawan yin maski koda basu shafa mai ba.


4- Canjawar sinadaran jiki; Akwai sindarai da yawa a jikin ɗan Adam, Canjawar wasu daga cikinsu zai iya kawo wannan matsalar. Misali, idan ƙaramin yaro ya fara balaga, zamu ga fuskarsa tana yin maski fiye da ƙima. 


5- Stress; Wato lokacin da jiki ya jigata da yawa, ta hanyar zurfafa tunani dake wahalar da ƙwaƙwalwa ko kuma wani aiki mai wahala, fuska ko nace fatar jiki takan rika tatso mai dake cikinta fiyeda lokacin da babu wannan wahalar. Zamu fahimci haka idan muka tuna yadda wasu suke fitar da zufa cikin hanzari duk lokacin suka shiga wani tashin hankali.


Wannan matsala ta maiƙon fuska ita ce take haddasa ƙurajen fuska a mafi yawan lokaci.


Wadannan sune kadan daga cikin dalilan dake sanya fatar jiki ta rika yin maiƙo fiye da ƙima. 
Domin ƙarin bayani ku duba shafukan  Lafiya Jari: 

Youtube

Facebook

Instagram

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-