Me ze faru da masu Amfani da wayar Huawei

 Bayanai da suke bayyana sabon processor da wayoyin Huawei zasu fara aiki dashi wanda Yasha banban da Android da IOS.
kamar yanda wasu daga cikin mu suka sani shine tin hawan Donald tromp Mulkin kasar america ya sakawa company Huawei na kasar china takunkumi ta yadda wannan company ze dena ampani da dukkan Abubuwan america wanda kowa yasan cewa kamfanin Google daya mallaki babban operating system din wayoyi na duniya wato Android na kasar america hakan Yasa wayoyin Huawei da suka zo shekaru uku da suka wuce musamman manyan irin jerin su mate da p zakuga basa taamuli da abubuwa na Google irin su YouTube Google play gmail da sauransu
Hakan yasa karbuwar da wayoyin suka samu yadan ragu a duniya sannan shikuma company karfinsa wajen bincike ya karu saboda ganin cewa cigaba da dogara da kayan wani ze iya bashi matsala a kowanne irin lokaci donhaka suka bazama wajen nemowa kansu mafita ta Yadda ba zasu dogara da wani ba a nan gaba da wasu daga cikinku zasu kula za kuga Yanda Huawei suka kirkiro play store dinsu me suna Huawei gallery app domin masu amfani da wayar suna dauko app a ciki.


Kirin 9010 Sabon processor daga company Huawei da karfinsa Yakai 3 nano mita
To bayan bincike me tsawo da aiki tukuru a kwanan ne company Huawei suka sanar da sabon processor dinsu me zuwa wanda sukace zaa saka masa suna kirin 9010 sannan sunce wannan processor ba zasu sakeshi ba se a jerin wayoyin su na Huawei mate 40wannan labari na sabon processor na Huawei yazo ne daga account daya daga cikin masu kula da harkar wanda ya rubuta a Twitter dinsa.

wannaan mataki da Huawei suka dauka ze temaka sosai wajan samu ci gaban gaggawa na wayoyin hannu saboda karuwar masu gasa hakan yana temakawa wajan samun canje canje kamar yanda muke gasa kowanne shekara tsakanin company Google da Apple akan operating system dinsu na Android da ios to idan Huawei ta bude nata kunga takara ze zama tsakanin mutun sannan gasar yin nasara zata karu wanda hakan zesa masu amfani suna samun sauye sauye da gaggawa.
Amma ku menene raayin ku game da wannan mataki da Huawei suka dauka na barin amfani da Android anan gaba kadan shin kuna ganin hakan ya dace ko yaya muna jiran raayinku agun comment


wassalam. 

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-