Muhimman Sirrikan da suka fito daga Kamfanin Android

Muhimman Sirrikan da suka fito daga Kamfanin Android

 


Muhimman Sirrikan da suka fito daga Kamfanin Android


Assalamu Alaikum warahmatullah yan uwa barkanmu da wannan lokaci. A yau da yardar Allah zamuyi bayani ne akan wasu sirruka(Applications) wanda yawancin mutane basa amfani dasu kuma Alhali suna da Amfani sosai, dan haka yau muka zakulo muku su domin su amfane ku.


Sunayen Applications din


Na farko : Muslim pocket
wannan Application ne mai matukar Amfani sosai, domin daga jin sunansa kasan ya shafi musulmai. Ana amfani da wannan Application din domin samin yawancin duk abinda musulmi yake bukuta a gaggawa shi yasa suka kirashi da muslim pocket, ma'ana Aljihun musulmi. Abubuwan da wannan Application din yake dasu.


1. zai fada maka lokutan sallah ko aca kasa kake
2. yana dauke da Alqur'ani mai girma, zaka iya karantawa kuma zaka iya ji, domin akwai karatun manyan malaman duniya
3. akwai sunayen Allah acikin sa
4. zaka ga duk abincin da yake halal da kuma wanda yake haram
5. zai nuna maka Alqibla a kowani guri kake


Da sauransu


Domin yin download dinsa danna nan


Download

Download


Na biyu : Super cloneWannan Application din yana da amfani sosai, domin zai taimaka maka gurin kara adadin duk wani Application da kake so. Misali idan kana da Facebook account da yawa kuma app daya ne dakai kaga dole sai kana login ko logout, Amma idan kana amfani da wannan Application din zaka iya yin copy din Facebook iya yadda kake so.


Somin download dinsa


Download

DownloadNa Karshe : BulldogWannan Application din anyi shine domin kula da tarbiyar danka ko yarka ko kaninka. Domin zai baka damar ka tsayar da  duk Applications din da baka so danka ya shiga ko kuma website din da baka so ya shiga. Dan haka wannan ma yana da muhimmanci sosai a gurin wanda yake kula da tarbiyya.


Domin yin download dinsa


Download

Downloadwannan shine karshen darasinmu na yau. W assalamu Alaikum.

Mungode. 

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-