AMFANIN WANKE HANNU GA LAFIYA
🔱Wanke hannu na daya daga cikin matakan farko wajen kula da lafiya.... Ya kan taimaka wajen kare afkuwa tare yaduwar cututtuka ta hanyar wanke qwayoyin cuta da suka taba hannu.
⚛️Yaushe Ne Ya Kamata Mutum Ya Wanke Hannuwanshi?!⚛️
⚜ Kafin, a yayin da, da kuma bayan hada abinci.
⚜ Kafin cin abinci.
⚜ Kafin kula da mara lafiya, da kuma bayan kula dashi.
⚜ Kafin, da kuma bayan da mutum ya taba rauni.
⚜ Bayan amfani da bayan gida (toilet).
⚜ Bayan an canjawa jariri pampas ko kuma bayan an saka yaro a toilet.
⚜ Bayan fyace hanci, tari ko atishawa.
⚜ Bayan taba dabbobi, abincin dabbobi ko gyara gurin dabbobi.
⚜ Bayan ta6a shara.
Domin ƙarin bayani ku duba shafukan *Lafiya Jari*:
*Youtube*:
*Facebook*:
*Instagram*: