Sabon whatsapp mai abun mamaki 2021

Sabon whatsapp mai abun mamaki 2021


Sabon whatsapp mai abun mamaki

 Assalamu Alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da warhaka, dafatan mun sake saduwa da ku cikin aminci.A yau da yardar Allah zamuyi bayani ne akan wani muhimmin Application wanda kowa yake amfani dashi, mai suna Whatsapp.

Bayani akan WhatsApp na Asali.

Kamar yadda muka sani ankirkiri WhatsApp ne a shekarun baya 24 - feb - 2009. Kuma yasamu amsuwa a gurin jama'a, a yanzu yana daya daga cikin Applicationa wanda akafi amfani dasu a duniya. Wanda mutane sama da billion 2 suke amfani dashi. Wannan Application na WhatsApp in kana sanshi ( in kana so kayi downloading na yan kasuwa mai suna WhatsApp Business. Duk su biyun suna da abubuwa na musamman wanda mai amfani dasu zaiji dadin aiki da su. Abu na karshe akan WhatsApp na asali shine, duk wasu bayananka zasu adana maka, ta yadda hackers bazasu iya cimma bayananka ba, sannan ba wanda zai kulle maka lanbar wayarka, musamman idan ka saka two-step-verification.

WhatsApp wanda bana asali ba (Na Bogi)

Bayan an kirkiri WhatsApp kuma akaga irin nasarar da ya samu, sai wasu daga cikin mutane suke kokarin su saci fikirar (fasahar) sa . Daga nanne aka kirkiri Gb WhatsApp, WhatsApp plus, da saurasu.

Suna da muhimmanci?

Ea suna da muhimmanci sosai, ta yadda zakuga akwai abubuwa da yawa wanda WhatsApp na asali bashi dashi amma su wadannan suna dashi, misali, themes, canza sunan sa, da sauransu. Zakayi wayanci duk abinda kake so a cikinsa. Dan Haka mutane da yawa suna Amfani da shi. 

Sanarwa

wannan whatsapp din bayayin installing a wasu wayoyin. kuma insha Allah mun kusa yin video akansa

Wannan shine link din:


Dannan nan


Mene matsalarsa?

Yana da matsalaloli da yawa, amma zan dauki masu muhimmanci nayi bayani akansu. 

Na farko Rashin tsaro

In kana amfani da WhatsApp wanda bana asali zaka iya samun matsalar satar bayanka, ina mufin hackers zasu iya daukar duk sakunnin da kake yi. Kuma su tuawa wanda suke so.

Na biyu zaka iya Rasa Number ka

Kamfanin WhatsApp na asali da suka fahimci mutane suna satar musu fasaha, sai suka dau matakin rufe duk wata number da take amfani da WhatsApp na bogi. Dan haka in kana amfani da shi, zaka iya rasa lambarka.

Ra'ayina

Zaka iya amfani dashi idan kana da lambobi ya yawa, saboda yana da abubuwa sosai a cikinsa. Amma idan lambarka daya ce kuma samun sabon layi abune mai wahala a gurinka to karkayi amfani da shi.
Yan uwa anan muka kawo karshen wannan darasinnamu na yau , dafatan ya burge ku kuma zai amfane ku. Kada ku manta dayi mana sharing na wannan page dinnamu.

Daga MUHAB TEAM

Wassalamu Alaikum.
Mungode.

Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-