Yanda zaka dau dukkan kalar Videon da kake so kuma da sauti mai kyau
Assalamu Alikum warahmatullah, yan uwa barka da warhaka sannunmuda sake saduwa daku a wannan sabon darasin.
Darasinmu na yau zaiyi bayani ne akan hanyar da zakayi amfani da wayarka kamar camrerar da take da mic, abinda nake nufi a nan wannan App din zai taimaka maka gurin daukar Sauti mai karfin gaske.
SUNANSA
Sunan Applicqtion din nan Dolby on, zaka same shi a play store amma ba a kowacce waya ce zata ganshi ba. Kuma wannan Application din yanzu haka a nanan ana ta kara masa abubuwa a cikinsa, domin wadanda zasuyi amfani dashi suji dadinsa sosai.
YADDA ZAKAYI DOWNLOADING DINSHI
Da farko zakaje play zaka rubuta sunansa (Dolby on) zai zo maka kamar haka. Masu wannan Application din basu yadda a dau link dinshi ba dan haka nabi wasu hanyoyi domin na kawo muku wannan link din. Amma na tabbata zaka ganshi indai kaje play store.
Wannan shine link din sa
AMFANINSA
Zai taimaka maka gurin daukar sauti mai kyau sosai, musamman ga youtubers wadanda basu da mic zasuji dadin Aiki da wannan App din. Wadanda suke son yin waka suma wannan Application din zai taimaka muku sosai.
DAGA KARSHE
Muna fatan Wannan Application din zai taimaka muku. Da wannan muke ce muku wassalamu Alaikum.
Mungode