Yanda zaka kare kanka daga hacking

 


Abubuwan daya Kamata kayi don ka kare kanka daga Hacking 



Da yawa daga cikin hacking din da suke faruwa suna faruwa saboda wasu sabuba kamar kuskure na mutum ko kuma ganganci dade saurarnsu , Yanzu haka muna shekarar 2021 idan baka koyi yanda zaka iya kare kanka daga masu hack bah to zaka iya wayar gari kaga har account dinka na banki anje anmaka sata cikin sauki.


Hacking yana daya daga cikin abubuwa masu hadari da suke fuskantar jamaa kamar irin wadanda suka faru a shekarar 2020 tare da shugaban America donald j trump ta yanda a kayi hacking din account dinsa na twitter ko kuma zoom din din da akayi wanda shugaban minister yayi , sannan muma akan kanmu abu je me hadari.

Donhaka a wannan bayani zamu kawomuku hanyoyi kadan da zasu temaka wajan kare accounts dinku daga hack .

Matakan kariya


Two step verification


Ya kamata ace mutum ya kunna two step a kowanne account dinsa saboda wannan hanya tana daya daga cikin manyan hanyoyin da su kafi kowanne hanyoyi temakawa account.


Password management


Da fari ya kamata ka sani cewa sanya password me karfi yana temakawa wajan rage zaton zaa maka kutse , amma saboda yanda social media sukayi yawa a duniya kuma kowanne yana neman password dole ya kasance mutum yana manta password donhaka amfani da wannan yana da matukar muhimmanci don kiyaye maka passwords dinka.

Kiyaye link 


Bayan zuwan cutar data bayyana a duniya ansamu hanyoyi masu hadari da ake amfani dasu wajan cutar da mutane ta hanyar link donhaka duk link din daka gani ya kamata ka kula dashi kafin ka danna shi .

Update kowanne lokaci


Duk applications din da muke amfani dasu tin daga kan irin su facebook har zuwa abin daya shafi OS suna fuskantar barazana ta kutse donhaka dukkan kamfanunuwa suke bincike akan kuskuren da zeja a iya shigomusu se suyi maganinsa donhaka ya kamata duk lokacin da company sukayi update na Application kaima kayi .

Goge tsofin account

Wannan hanya ce da masu kutse suke amfani da ita sukan je su nemi tsoffin account da mutum ya dena aiki dasu su tattara bayanan su ta hanyar wadannan bayanai se su kokarin yi masa hacking .


Wadannan sune hanyoyin a takaice donhaka semu kula sosai .

Domin gwada password dinka 


Mungode 


Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-