Alhamdulillah|| Daga yau ba wanda ya isa yaga wayarka

 
Alhamdulillah|| Daga yau ba wanda ya isa yaga abinda yake a wayarka


Alhamdulillah|| Daga yau ba wanda ya isa yaga abinda yake a wayarka


Assalamu Alaikum yan uwa barka da warhaka sannunmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a darasinmu na yau zamuyi bayani ne akan yadda zaka kare sirrin wayarka ta yadda bawani Application da zai kara cutar da kai.


Sunan Application Sunansa (paranioa access) , zaka same shi a play store, kuma bashi da nauyi kwata-kwata. Wannan Application din bai dade da fitowa ba, Sama da mutum dubu goma ne sukayi downloading dinsa, Dan haka na tabbata da kaima zaka ji dadin Amfani dashi.


Mene Amfaninsa


Amfanin Wannan Application zai taimaka maka gurin sanar da kai duk wani Application da yake daukar maka sirrinka a boye, saboda da yawa akwai wasu Application da suke daukar sirrikan mutane a boye kamar suringa daukar photonka ko videon abinda kake yi ko kuma suna recording din duk wayar da kake yi , dan Haka idan kayi amfani da wannan Application din zai sanar da kai duk irin wadannan Applications din.


Ga wanda yake son yayi download dinsa


Download

Download

Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.


Yanda zakayi Installing dinsa

Zakaje play store kayi download dinsa. 

Bayan ka gama download dinsa kai tsaye zaka shige shi, zai tambaye ka ka bashi damar aiki a wayarka  bayan ka bashi damar kai tsaye zaka fara amfani dashi. 


Dafatan kunji dadin wannan darasin , kuma insha Allah zai amfane ku.

Mungode.

Wassalamu Alaikum.

 


CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-