Babban Sirrukan Waya ( ya kamata kowa yayi Amfani da shi)
Assalamu Alikum yan uwa barka da wannan lokacin, a wannan darasin namu naa yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application wanda ya kamata kowa yana Amfani dashi, domin zai taimaka maka gurin Tsara wayarka ta zama kamar yau ka siye ta. (Na tabbata sai Burge ka).
Application me suna Taskbar
Yan uwa assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin dake kawo muku manyan application na zamani.
Ayau zamuyi takaitaccen bayani kan wasu shahararrun applications na wayar hannu ta Android.
Daga cikin jerin wannann apps din akwai na farkonsu me suna Taskbar kamar yanda muka fada.
Wannan application din yana taimakawa wayarka wajan shirya ragowar application tare da daidaitasu a waje guda tamkar a cikin computer ko kuma nace tamkar ansakawa wayarka windows 10.
Saukin dakkowa da saurin da yake sakawa wayar Android yasaka mukazo da wannan app.
Kawai abinda zakai da zaran ka sauke wannan app din ka jawo screen din wayarka a gefen haugnka zakaga wani waje an rubuta (Freeform) kana dannawa ze kaika wajan setting seka kuna,daga nan zakaga abun biyan bukata a wannan app din.
Domin dakkoshi Danna nan
Yanda zakayi Download dinsa
Zakaje play store kayi download dinsa.
Bayan ka gama download dinsa kai tsaye zaka shige shi, zai tambaye ka ka bashi damar aiki a wayarka bayan ka bashi damar kai tsaye zaka fara amfani dashi.
Dafatan kunji dadin wannan darasin , kuma insha Allah zai amfane ku.
Mungode.
Wassalamu Alaikum.