scholarship a kasar waje

 


scholarship ta karatu kyauta


Assalamu alaikum warahmatullah barkanmu da sake saduwa daku

Bayani akan scholarship din kasar Libya ta jamiar international slamic call collage wanda take a kasar Libya

Bayani akan jamia

Wannan jamiaar Tana a babban kasar libya wato tripoli takai sama da shekaru daruruwa da bude tin a lokacin take yaye dalibai daga kasashen funiya daga kowanne bangare tin daga kan Asia Africa da kuma Europe da America, makaranta ce me dunbin tarihi da aka santa a duniya baki daya kuma certificate dinta ana mutuntashi a kasashenmu .

Ita wannan makaranta komai a cikinta kyauta neh tin farkonta idan ka samu admission komai su zasuyi maka tin daga kan visa harma da ticket din jirgi da komai zasu turomaka hargida sannan anan komai zaa baka kamar gun kwana da abinchi da komai.

Faculties

Bangarorin da ake dasu a wannan makarantar Yanzu haka sune kamar haka

Bangaren addini

Islamic studies
Sharia and Law
Islamic daawah
Arabic Language

Bangaren Boko

Computer science
Imformation tech
Banking and finance
Accounting

Cikakken bayanai akan wannan makarantar 


Yanda zaka nemi admission


Cikin sauki zaka turamusu takaddunka ta email dinsu babu shan wahala

Ga Email din : admission@uic.edu.ly

Ga videon da zaka kalla ka koyi yanda ake tura takaddun


Sharudan Neman admission da takaddun da ake nema wajan Apply

Sharuda

Ya kasance kana da takaddar secondry
Ya kasance kana da passport
Sannan kada shekarunka su haura 23
Sannan ya kasance baka da cutar da ake goga

Takaddun da ake so

 • Wasika zuwa ga shugaban makaranta
 • Certificate dinka na secondry
 • Stamp na ministry of forein affairs
 • Stamp na ministry of Education
 • Police report
 • Passport da zekai shekara 3
 • Kananun hoto
 • Wannan sune takaddun a takaice wassalamu alaikum

  Comments  Font Size
  +
  16
  -
  lines height
  +
  2
  -