Yanda zaka bude whatsapp da lambar America

 


Yanda zaka bude whatsapp da Lambar America


Assalamu alaikum warahmatullah 

En uwa barkanmu da sake saduwa daku a wani sabon sharhi a blog din www.muhabteam.com

Kamar Yanda kuka gani a sama Yau zamu koya muku Yanda zaku iya kirkirar whatsapp da Lambar kasar Amurka kuna zaune a kasashenku a kowacce kasa kuke a duniya kuma koda kuwa ina mutum Yake zeyi Amfani da ita Ta hanyar Amfani da Application din Talkatone.

Menene Talkatone

Shi TalkaTone Application neh da yake bawa Mutum dama Ya mallaki lambar kasar Amurka domin yayi kira ko a turomasa sako ko kuma kiran waya ko kuma dukkan abin da ake da lamba a duniya shima yayi Talkatone ya kasance kamar kowanne Application a wannan duniya.

Yaya ake bude whatsapp din kasar waje dashi 

Yanda ake bude whatsapp din kasar waje dashi da fari mutum ze bude account a wannan application bayan nan ze nemi lamba bayan ya zabi lambar da ta masa ta kasar Amurka zeyi amfani da ita wajan ya bude whatsapp se yasa whatsapp su kirashi daga nan sesu bashi pin daga sesu bude whatsapp da wannan Lamba.


Shin Ana amfani da wannan application Sama da miliyoyin jamaa neh suke amfani da wannan Application me matukar farinjini saboda Yanda kowa yake biyamasa bukatarsa kuma yana da matukar saukin Amfani.


Wannan shine cikakken bidiyon Yanda ake bude whatsapp

Yanda zaayi download wannan Application a google play jamaa da yawa suna nemansa amma ana cemusu babu shi a kasarsu to Abin da yake faruwa wannan Application yama da wuyar samu donhaka na kawomuku link din download cikinsauki kawai kudannan kalmar download tanan kasa


Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Mungode da bibiya wassalamu Alaikum

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-