Yanda zaka gano sirrukan kowace waya a wannan duniyar
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barka da wannan lokaci, a darasinmu na yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application Wanda zai taimaka maka gurin siyan Wayar da tafi dace wa ka siya.
Ya sunan Application din?
Sunansa mobilist, yana da matukar amfani gashi bashi da nauyi kwata-kwata bai wuce MB 30 ba , sannan sama da mutum dubu dari ne suka dakko shi 100k+, Dan haka na tabbatar da kaima zaka ji dadin Amfani dashi domin kana bukatarsa a kowani lokaci.
Mene Amfaninsa (Mobilist)
Amfanin wannan Application din mai suna Mobilist zai taimaka maka gurin siyan waya mai karko, Amma bari nayi maka cikakken bayani.
Abinda yake yi shine
1. Zai baka damar siyan wayar da tafi dacewa da kai
Abinda nake nufi anan, watakila kana so kasiyi waya amma bakasan wani kamfani ne yafi ba misali samsung ko Iphone , zakayi amfani da wannan Application din domin ya ban-bance maka tsakaninsu sannan ya fada maka wacce tafi.
Wani lokacin kana so kasiyi waya ne domin camera, zakayi Amfani da wannan Application din domin ya nemo maka wayar da take da camera sosai.
Watakila wani Ram yake so da yawa , wani kuma Storage yake so da yawa: duk bukatar ka zaka iya nema a wannan Application din.
2. Zai sanar da kai Idan wani kamfanin yazo da sabuwar waya.
Duk lokacin da samsung ko Iphone suka fitar da sabuwar waya toh wannan Application din zai sanar da kai, kuma ba dole ne sai Samsung ko Iphone ba , koda Itel ko Techno ko Infinix idan suka fitar da sabuwar waya wannan App din zai sanar da kai sannan ya fada maka Farashinta.
yana da yawa , domin gane wa idan ka kayi download dinsa
Domin yin download
Wassalamu Alaikum.
Mungode.