Yanda zaka kirkiri sabuwar waya acikin wayarka (yana aiki 100%)

 Yanda zaka kirkiri sabuwar waya acikin wayarka (yana aiki 100%)




Assalamu Alaikum warahmatullah, yan uwa barka da warhaka sannunmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin. A yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda ya kamata kowa ya sansa. Domin na tabbata kana ganinsa zai matukar burgeka.


Mene sunan wannan Application din?


Sunansa (f1 vm lite). Wannan Application din zai baka damar kirkirar wata sabuwar waya acikinsa kuma wayar Android. wani zai iya cewa hakan ai ba zaiyyu ba, Nima kafin na gano shi haka zance amma tunda kuka ga na kawo muku shi to tabbas zaiyi wannan Aikin. Domin saida na gwada shi sannan na kawo muku shi.

zaka same shine a play store, dubunnan mutane ne sukayi downloading dinsa. Dan haka kaima zaka iya jarraba shi watakila ya burge ka.

Abubuwan da zaka iya yi acikisa

1. Installing na kowani kalar Application
2. canja tsarin waya
3. Downloading kowani kalar video. komai da zaka iyayi a wayarka zaka iyayi a wannan Application din


Domin downloading dinsa


Danna Nan
Danna Nan
Danna Nan


Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Yanda zakayi downloading din wannan babban Application


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.

Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .

Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.



Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-