yanda zaka san sirrin kasuwancin youtube
Assalamu Alaikum yan uwa barka da warhaka sannun mu da sake saduwa da ku a wannan sabon darasin. A wannan darasin kamar yadda kuka gani zamuyi bayani ne akan hanyoyin da zasu taimaka maka gurin masun kudi da yawa a YouTube.
Akwai website da yawa dasu taimaka maka gurin cimma burinka na samun kudi da yawa, amma kafin nayi nisa a bayanin dole ne kasan me yasa ake samun kudi a YouTube.
Me yasa ake samun kudi a YouTube?
Abinda yasa ake samun kudi a YouTube, youtube suna samun damar dora talla a videon, kuma baza'a fara dora talla ba dole sai kana da mabiya wanda suke kallon videon ka. 4000 hours view da subscribers dubu daya 1k.
kunga ke nan burinsu mutane, domin su zasu ga tallan. Dan haka yazama dole musa mutane suna kallon videos dinmu.
Wata hanya zaka bi domin ana kallon videos naka??
1. Kana yin videos wanda zasu ja hankali
2. Sannan kana amfani da mic mai kyau domin ya fidda sauki mai inganci
3. kana yin thumbnails masu kyau
Mene ne Thumbnail
Thumbnail shine hoton da ake dorawa akan videos domin ya ja hankalin mutane domin su kalli videon.
ya ake hada thumbnail
Anan hada tane a photoshop ko powerpoint ko coral draw da sauransu. Amma yanzu akwai Application wanda zasu na taimaka maka gurin gurin yin thumbnail a saukake.
Canva
Akwai wani website mai suna Canva, zai taimaka maka gurin yin designed na kowani abu da kake so. Asalinsa na kudi ne amma mutum zai iya amfani da shi a free, kuma zaka iya canja shi zuwa duk yaran da kake so, kuma koda hausa ne.
Wannan shine link din Downloading na Canva
In baza ka iya amfani da Canva ba zaka iya shiga wannan website din domin dakko duk thumbnail din da ta burge ka a YouTube.
Wannan shine link din website
Inkayi amfani da wannan hanyar da yardar Allah zaka na samun view sosai a channel dinka, in ka zamu views kaga zaka samu kudi ke nan.
Samun kudi ta hanyar hurda da Kamfanoni ( Spansors)
zaka iya samun kudi masu yawa idan kana hurda da kamfanini, ma'ana su baka tallan kayansu. bazaka cimma wannan burinba dole sai kana da mabiya da yawa. dan haka dole ne ka bi hanyar da zaka samu mabiya sosai, domin dasu ne zaka samu kudin.
Insha Allah a darasinmu na gaba zanyi mana bayanin hanyar da zaka ga ko nawa mutum yake samu a YouTube, kuma zaka iya ganin na kowacce channel.
Anan nake ce muku wassalamu alaikum.
Mungode.