Application na kamfanin Google mai suna Flies
Wannan Application din zai ajiye maka duk wasu sirrukanka ko kuma nace duk wasu flies dinka, sannan zaina lissafa maka komai, sannan zai baka damar tura duk abinda kake so ba tare da xender ba.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Wannan wani Application ne
Sunansa (Google flies) wannan Application din mutane sama da miliyan dari ne sukayi downloading dinsa kuma bashi da nauyi kwata-kwata baifi 10MB ba.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din ya fito ne daga wannan babban kamfanin wato kamfanin Google.
Amfaninsa a takaice shine zai baka damar adana bayananka a cikin kwanciyar hankali, sannan zaina lissafa maka komai, misali adadin videos, adanin Audio, adadin photos da sauransu sannan zai baka damar tura duk abinda kake so ba tare da xender ba. Domin kun san cewa a lokacin da mutane suke ture ture a wannan lokacin akan iya satar maka bayanai. Dan haka wannan Application dinne mafi dacewa domin duba komai na wayarka.
Wannan Application din na musamman ne , ya kamata kayi amfani dashi.
Domin downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.