Babban cigaban da aka samu a wannan shekarar
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan wani babban Application wanda zai dau photon wanda ya satar maka wayarka. Sai ya tura maka cikin Email dinka.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Amfanin Wannan Application din
Ankirkiri wannan Application dinnan ne domin taimaka wa mutane gurin Amfani da wayoyinsu na hannu, domin abinda wannnan Application din zai maka ba karami bane kuma a free.
A takaice aikin wannan Application din zai maka babban Amfani domin zaina daukar photon duk wani mutum da ya taba maka wayarka, sannan ya tura maka cikin Email dinka.
Idan wataran an sace maka wayarka , idan wannan barawon da ya dau wayar yayi kokarin budeta to yana dannawa wannan Application din zai dau photonsa sannan ya turo maka . Kaga daga nanne zaka gane wanda ya satar maka wayarka.
Domin downloading din App na farko
App na biyu
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.