Yadda zakayi amfani da Google lens
Wannan wani keyboard ne wanda zaiyi maka komai wanda akwai komai a cikinsa, kamar imogies, stickers da sauransu.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Wannan wani Application ne
Sunansa (Gboard) wannan Application din mutane sama da miliyan dari ne sukayi downloading dinsa kuma bashi da nauyi kwata-kwata baifi 30MB ba.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din ya fito ne daga wannan babban kamfanin wato kamfanin Google.
Gboard yasha banban tsakanin sauran keyboard domin zai baka damar yin searching a google kai tsaye batare da kare cikin brawser ba.
Bayan haka wannan keyboard din yana da duk wasu abu da kake bukata su a lokacin rubutu, sannan zaka iya kara mai girma ko rage shi. Yana da abubuwa da yawa wanda ya kamata ka sani, amma idan kayi downloading dinsa zaka gani da kanka.
Dan haka Wannan Application din na musamman ne , ya kamata kayi amfani dashi.
Domin downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.