Yanda za kayi amfani da google keep
Assalamu alaikum warahmatullah en uwa barkanmu da sake saduwa daku a wani darasi
Kamar Yanda kuka gani a sama zamu muku bayani ne akan wami muhimmin application da yazo daga babban kamfanin technology wato google na wani application dinsa me matukar muhimmanci wato keep
Amfanin wannan application
Shi wannan application na keep babban muhimmancinsa agun dan adam shine ze saukaka masa rayuwar sa wajan kula da alamuransa na yau da kullum akan abubuwan da suka shafi rubuce-rubuce ta yanda duk abin da kakeso ko kuma ka gani ko kuma kakeso kayi zaka iya rubuta shi a wannan application din.
Daga cikin abin mamakinsa
Bayan ka rubuta abin da kakeso kayi a jikin app dinnan zaka iya bawa application din lokaci ta yanda in lokacin yayi ya tinamaka da wannan abun da zakayi
Ko kuma zaka iya bawa application din location ta yanda daga kaje dede wajan ze tinamaka abin da kakeso a wajan
Temakon da app dinnan ze maka
Ze takaita maka lokacin ka
Ze saukaka maka rayuwa
Ze baka lokaci da yawa
Ze sa ka dena manta abubuwa
Zesa kana yin abubuwanka a tsare
Ze hana ka manta komai
Muhimman cinsa suna da yawa sosai amma zamu takaita anan
Wannan application din idan ya burgeka sosai za kayi download dinsa a kasa ga link din .
Wannnan shine karshe mungode kada ku manta da shere da kuma comment.