Yanda za kayi kowanne kalar lissafi cikin sauki
Assalamu alaikum warahmatullah en uwa barkan mu da sake saduwa daku a wannan darasi da muke kawomuku wani application me matukar muhimmanchi
Me application din ya kunsa
Application din da muka kawomuku yau yana da matuqar muhimmanchi ga duk wani dalibi da yake son koyon karatu ko kuma yake makaranta ya keso yana iya math matics .
Tsarin Yanda app din yake
Da fari zaka dauki littafi zaka rubuta dukkan tambayoyin da kake dasu a takadda amma ka tabbata rubutun zaa ganeshi daga nan kawai se ka shiga app din daga nan se kayi scanning din tambayar shi kuma application din ze bayyana maka amsar maana ze nemo maka yanda amsar take
Abin da ze burgeka da wannan app bayan ya nuna maka amsar kai tsaye ze nuna maka hanyar da yabi ya samu wannan amsa wanda hakan ze baka damar kaima ka koya kaga riba biyu kenan ya temake ka kuma ya koya maka .
Yanda xaka yi download din wannan app
Idan bayani da tsarin wannan app sun burgeka kaga ya kamata ka dauko shi to hanyar tana da matukar sauki zaka yo kasa za kaga kalama da alamar ruwan omo an rubuta download ka danna ta zata kaika gun download din app din
Wannan shine karshen darasin idan ya burgeku kada ku manta da shere da like mungode