Yanda zaka dawo da duk hoton da ka rasa ko ka goge
Assalamu alaikum, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai.
Wannan wani Application ne
Sunansa (Disk digger ) wannan Application din mutane sama da miliyan 100 sukayi downloading dinsa kuma bashi da nauyi kwata-kwata.
Mene amfaninsa
Sauda yawa mutane sukan rasa photos dinsu a wayoyinsu, idan aka sace musu wayarsu ko idan ta bata. A wannan lokacin zakaga mutum ya fara mutanin ta wacce hanya zai dawo da hotunansa!? Idan kayi amfani da wannan Application din zai dawo maka da duk photos din da ka taba gogewa a wayarka ta hannu. Kuma wani abu mai dadi akan wannan Application din shine bashi da wahalar amfani kwata-kwata, kana dakko shi zaka fara amfani dashi a saukake.
Domin downloading din na free
Domin downloading din na kudi
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.