Yanda zaka gyara kowani kalar video ya zama karami
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Wani Application ne wannan
Dafarko Sunansa (video compressor) zaka same shi a play store , dan mutane da yawa sunyi amfani dashi kuma bashi da nauyi kwata-kwata, zan ajiye muku link dinsa a kasan wannan rubutun.
Mene Amfanin wannan Application din?
Wannan Application din ya shahara gurin kwan-kwantar da video mai MB da yawa zuwa dan karami. A takaice wannan Application din zai rage maka girman videonka zuwa dan karami, misali kana da videon da yake da girman 100MB idan ka sakashi a cikin wannan Application din zai iya dawowa 10MB ko 20MB. Kai tsaye zakayi amfani dashi a duk inda kake so. Ina fatan zaku jarabashi domin yana da muhimmanci.
Domin downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.