Yanda zaka gyara photonka (Photo Editing)
Assalamu alaikum, yan uwa barkanmu da sake sasuwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani Application da zaina gyara maka photonka domin yayi kyau sosai.
Wannan wani Application ne?
Sunan wannan. Application din shine (ToonApp). Yana nan a play store, sama da mutum miliyan biyar ne suka dakko shi, kuma bashi da nauyi kwata-kwata 22MB.
Mene Amfanin ToonApp
Amfanin ToonApp shine zai baka damar canja photonka, ta yadda zaiyi kyau sosai. Amma wannan Application din na kudi ne amma mu zamuyi amfani dana free domin wasunmu da yawa baza su iya siyan na kudi ba dan haka kai tsaye dana free zamuyi amfani dashi.
Zai maida maka photonka kamar haka
Yanda zakayi Amfani dashi
Kai tsaye zaka fara amfani dashi bayan kayi installation dinsa. Amma idan kana son cikakken bayani akan wannan Application din to ka kalli wannan videon.
Domin downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.