Yanda zaka boye sirrukanka na waya wannan babban cigaba ne



Yanda zaka boye sirrukanka na waya wannan babban cigaba ne


A wannan darasin zamuyi bayani ne akan wani babban Application wanda zai boye maka dukkanin surrukanka na wayarka ta sabuwar hanya.

Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.

Amfanin Wannan Application din


Ankirkiri wannan Application dinnan ne domin taimaka wa mutane gurin Amfani da wayoyinsu na hannu, domin abinda wannnan Application din zai maka ba karami bane kuma a free.

A takaice aikin wannan Application din zai baka damar boye sirrukanka misali kamar photos, videos da duk wani file.

Bayan haka zaka iya boye applications dinka na kan wayarka, dan haka bawani wanda ya isa yaga wani Application din da baka so baka so ya gani. 

Akwai saitawa zakayi, bayan ka saita zai boye maka komai a saukake.
 

Domin downloading dinsa



Yanda zakayi downloading din wannan babban Application 


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.

Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .

Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.
Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-