Application din da zai taimaka maka a Ramadan
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan yadda zaku na iya tura komai a wayarka ba tare da kayi amfani da bluetooth ko Xender ba, kawai zakayi amfani da wani sabon Abu.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani a watan Ramadan.
Karamin bayani akan wannan
Sunan wannan Application din (Tarteel), zaka same shi a play store kuma sama da mutum dubu hamsin ne suke yi amfani dashi, dan haka kaima zaka iya jin dadin amfani dashi.
Amfaninsa
Wannan wani Application ne wanda zai taimaka maka gurin yin Azumin watan ramadana cikin jin dadi.
Zakayi amfani da wannan application din wajan gano kowacce sura ba tare da kasan wata sura bace. Misali idan kana tafiya kawai sai kaji ana karanta Alqurani, kuma kai baka san waca sura ba ce , amma idan kana amfani da wannan Application din kai tsaye zaka kunna shi, shi kuma zai gaya maka wace sura ce kuma zai baka damar ci gaba da karantawa.
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.