Yanda zaka gano wayarka da aka sace ta hanyar ( FITO)
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, dafatan kuna lafiya.
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan wani Application wanda zai baka damar gano wayarka da aka sace ko ka nemeta ka rasa ta hanyar yimata fito da baki!
Mene Amfanin wannan Application din?
Da farko wannan App din halastacce ne, domin kuwa yana nan a cikin wajan dauko app na google Playsrore.
Kadan daga cikin amfanin wannan App din wasu lokutan mukanje gidan biki ko wajan wani taro, kaga an zare wayarmu a Aljihu ko kuma a sace mu rasa wanene ya dauka ko ta yiwu munajin kunyar caje wanda muke zargin sun dauka.
A dan haka wannan App din yazo mana da hanya mafi sauki da idan muka saka shi kai tsaye zamuyi mata Fito da bakinmu! Nan danan zakaga ta fara Ring wato sauti yana tashi tare da haske.. ta yanda koda wanda ya dauke ta ya sakata a fly mode ko ya zare Sim wannan app din yana iya tona shi.
Ba iya wannan abun wannan App din yake ba, kai harma wataran idan ka aje wayarka ka manta inda ka aje zaka iya kiranta da bakinka kai tsaye ta fara kara.
Sauki da rashin nauyin wannan App din yasa mukai amfani dashi domin jin dadinku
Amma wannan application din zai taimake ku sosai kuma zai burge ku. Zaka gane shi sosai idan ka kalli wannan videon.
Dan haka ina da tabbacin cewa wannan Application din zai burge ku. Domin dakko wannan babban Application din zaka ga guri an rubuta Download.
Domin downloading dinsa
Domin kallon cikakken bayanin shi ka kalli wannan videon.
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.