Yanda zaka karawa tsayin story na whatsapp dinka
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan wani Application wanda zai baka damar kara tsayin status dinka na whatsapp.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, dafatan kuna lafiya.
Mene Amfanin wannan Application din?
Da farko sunan wannan Application din (video splitter for whatsapp) zaka iya samun shi a play store, kuma mutane da yawa suna amfani dashi kuma bashi da nauyi kwata kwata dan baikai MB 2 ba.
Kamar yadda kuka sani a whatsapp status baa dora abinda ya wuce second talatin.
Amfaninsa shine zai baka damar dora video ko Audio a status dinka na whatsapp wanda yafi second 30, zai baka damar kowani video kuma duk tsayin shi indai bai wuce kaida ba.
Dan haka ina da tabbacin cewa wannan Application din zai burge ku. Domin dakko wannan babban Application din zaka ga guri an rubuta Download.
Domin downloading video compressor
Domin downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.