Yanda zaka gano wanda yake bibiyarka a wayarka
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan wani Application wanda zai baka damar nuna maka wanda yake bibiyar ka a wayarka.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, dafatan kuna lafiya.
Mene Amfanin wannan Application din?
Da farko sunan wannan Application din (Access dot) zaka iya samun shi a play store, kuma mutane da yawa suna amfani dashi sosai kuma bashi da nauyi kwata kwata dan baikai MB 10 ba.
A wannan Application din zaina nuna maka duk wani Application da yake yi maka amfani da yawa, domin akwai wasu application wanda suke amfani da camerar ka, amma idan kana amfani da wannan application din zai nuna maka duk Application din da yake daukar bayananka.
Amma wannan application din zai taimake ku sosai kuma zai burge ku. Zaka gane shi sosai idan ka kalli wannan videon.
Dan haka ina da tabbacin cewa wannan Application din zai burge ku. Domin dakko wannan babban Application din zaka ga guri an rubuta Download.
Domin downloading dinsa
Domin kallon cikakken bayanin shi ka kalli wannan videon.
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.