Yanda zakana yin whatsapp da number america
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, dafatan kuna lafiya.
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan wani Application wanda zai baka damar yin whatsapp da number kasar waje, misali america
Abubuwan da kake nema?
Da farko kana da bukatar ka dakko wannan Application din mai suna (Arrow vpn) nashi da nauyi kwata kwata baikai MB 10 ba.
Domin dakko shi danna nan (Download)
Daga nan sai ka dakko Application mai suna (Textme) shima bashi da nauyi amma kafin ka dakko shi dole ne sai ka bude Application na farko (sai yayi connecting) sannan zaka dakko wannan na biyun.
Bayan ka dakko shi sai ka danne application din zaka ga guri an rubuta Info sai ka shiga daga nan zaka ga guri an rubuta permissions nan ma sai ka shiga ka bayan ka shiga sai kabawa komai na gurin dama.
To bayan ka gama komai sai ka shiga wannan Application din to acikinsa ne zaka sami number da zaka yi amfani da ita.
Domin dakko wannan Application din
Sai application na uku mai suna (Dual space lite) shi wannan bashi da nauyi kuma yana da amfani sosai.
Nasan a wannan bayanin ba lallai bane kun gane komai. Domin kallon cikakken bayanin akan yadda zaka bude whatsapp da number america ka kalli wannan videon, anyi shine da yaran Hausa.
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
(Babu nan)
Yanda zakayi downloading dinsu wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.