Kamfanin Huawei sun kirkirowa duniya sabon cigaba

 


Kamfanin Huawei sun kirkirowa duniya sabon cigaba


Assalamun alaikum, yan uwa barkanmu da wannan lokaci, a yau zanyi mana bayani ne akan wani cigaba da yazo duniya, dan haka kubini har karshen wannan labarin domin sannin wannan cigaban.


Series SF7Wannan wata mota ce wacce kamfanin Huawei zai fitar da ita a tsakiyar wannan shekarar. Wannan motar tana da abubuwan mamaki da ban Al'ajabi. Kudinta baya wuce tsakanin $50,000 zuwa $70,000.


Na farko :Ba'a sa mata feturWannan motar Electric car ce ma'ana mai amfani da wutar lantarki ce,


Na biyu : Sauki


Wannan motar tana da sauki gurin amfani da ita saboda (smart car) ce ma'ana zata iya kula da kanta, har ma ta tuka kanta ba tare da wata matsala ba.


Na uku : Ba fargaba (safe)Kamar yadda mukayi bayani wannan motar zata iya tuka tanta, bayan haka zata na nuna maka hanyar da tafi dacewa abi, da kuma yanda ya kamata ka tuka ta.

Kuma idan accident zai faro wannan motar zata taimaka maka gurin karkaji Rauni sosai.


Na hudu : Karfi


(684 horsepower) wannan motar tana da karfin doki sama da 684 dan haka zatayi gudu sosai.(A takaice)


Wannan motar zata fito a tsakiyar wannan shekarar, kudin ta bai wuce $70,000 , Electric car ce, zata taimaka gurin gyara mahalli, zata taimaka sosai gurin rage hatsari.Yan uwa mene Ra'ayinku dangane da wannan motar mai abun Al'ajabi???

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-