Yanda zaka gane duk matsalar wayarka
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani mai suna (Device info) a sama, wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Wannan wani Application ne?
wannan App din ze taimaka mana yayin da zamu sayar da waya ko kuma zamu saya, domin kuwan da zaran ka sauke wannan App din ze dauke dukkan wasu abubuwa na cikin wayarka ya dunkule su baki daya, ta hanyar nuna maka su a tsare a cikin sauki domin gane komai a cikin wayarka. awasu lokutan mukan so mu gano kyan batir din wayarmu ko kuma kyan Camera ko wani abun daban yan uwa wannan App din yanada abubuwa da dama zaka iya sauke shi ka duba abubuwa masu amfani wanda bamu zayyano su ba.
kuma wannan Application din bashi da wuyar Amfani, acikin sauki zakayi amfani dashi.
Na tabbata da wannan Application din zai burge ku.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.